Agwada Birni

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Agwada Birni

     G/WaÆ™a: Haba yara,

    : Mu koma Agwada ya hix2

     

     Jagora: Tun ban je Agwada ba,

    : Ana labarin Agwada birnix2

    : An ce Agwada dawa,

    : Kuma an ce agwada gero,

    : An ce Agwada ilmi,

    : Kuma sun ce Agwada maiwa,

    : Sun ce Agwada naira,

    : Kuma an ce Agwada shanu.

     

    Jagora : Haba yara,

    : Mu koma agwada birni,

    : Da na je Agwada,

    : In gwada masu,

    : Waƙa da kiɗa tsintsa[1],x2

    : Mutanen Agwada sun gwada,

    : Muna aikinsu zuwa gona.

     

      Jagora: Da naje Agwada na É—aya,

    : Sai ga dame É—ari,

    : Had da bakwa daidai,

    : Suka bai wa bahago Sani,

    : Kuma ga wan tauzan[2] ka riƙa,

    : Saboda nono da suga kullun.

     

      Jagora: Cikon na biyu,

    :Na koma zuwa hira,

    : Sai ga dame É—ari,

    :Had da bakwa daidai,

    : Suka baiwa Bahago sani,

    : Kuma ga wan tauzan ka riƙa,

    : Saboda nono da suga kullun.

     

     Jagora: Kuma na ukku,

    : Na sake zuwa hira,

    : Sai ga dame É—ari,

    : Had da bakwa daidai,

    : Suka baiwa Bahago Sani,

    : Kuma ga wan tauzan ka riƙa,

    : Saboda nono da suga kullun.

     

     Jagora: Ba ni koma zuwa gona.x2

    : Na huta da yini rana.

    : Idan na ji yunwa Agwada niy yi.

    : Ko ba ni ba,

    : Ni mai waƙa da kiɗi Sani,

    : Ko kai ka ji yunwa,

    : A gwada maka hanyar,

    : Agwada birni,

    : Da ka je Agwada,

    :Su gwada maka shago,

    : Da dawon[3] gero,

    : Da nono da suga kai É—ai.

     

    Jagora: Haba yara,

    : Mu koma Agwada birni.

    : Yaƙi noman sarki,

    : Inji Sani bahagon Inno,

    : Aikin tafiya,

    : Falke aka bar ma da mutane nai,

    : Yaƙi noman sarki,

    : Inji Sani bahagon Inno,

    : Aikin tafiya,

    : Falke aka bar ma da mutane nai,

    : Sha’anin duniya,

    : Kowa ya bi hanyar da yake tsira,

    : Sha’anin duniya,

    : Kowa yabi hanyar da take kai,

    : Ko waƙ ƙi ka da ɗa,

    : Ya gane ka da jikanka

    : Kana tawai[4],

    : Kuma baya da halin,

    : Ya taɓa ma shi.

     

      Jagora: Sha’anion duniya,

    : Kowa da masoyinsa yake kuri

    : Ko Mamman da masoyana.

     

    Jagora: Sha’anin duniya,

    : Kowa da masoyinsa yake ƙarya,

    : Ko Mamman da masoya na,

     

    Jagora: A bayar a rasa,

    : Ita ke hana yaro kaji motsi nai,

    : A bayar a rasa,

    : Ita ke hana raggo kaji motsi nai.

    : Allah waddan samun raggo,

    : Bai ci ba bai sha ba,

    : Bai tcere ma abokai ba.

     

      Jagora: Haba yara,

    : Mu koma Agwada birni.

    : Amadu rikiji É—an Cindo.

    : Amadu rikiji na gode ma,

    : Zakin Agwada ka biya[5],

    : Ka taimaki gangata.

    : Ina É—an mutuwa?

    : Yara ina ÆŠan mutuwa Ada?

    : Mai fetur mutumin Sani.

    : Sale ÆŠan Maidaji,

    : Allah ya kiyaye ka.

    : Sale É—an Maidaji,

    : Ka taimaki gangata.

    : Sarkin maƙera na gode mai,

    : Allah ya kiyaye ka.

     

     Jagora: Musa na Sale,

    : Allah ya kiyaye ka.

    : Na Binta a gaishe ka,

    : Sannu na Saratu na gode ma,

    : Baban Saratu ka kyauta,

    : Ka kyauta ma ƙanen Inno,

    : Yada kai mani,

    : Ka taimaki[6] gangata.

     

      Jagora: Alhaji Sani ÆŠanÆ™wari,

    : Allah ya kiyaye ka,

    : Sannu na Balki,

    : Ka taimaki ganga ta.

    : Haba yara,

    : Ku koma Agwada ya fi.

    : Yaƙi noma sarki,

    : Inji Sani bahagon Inno.x2

    : Aikin tafiya,

    : Falke aka barma da mutane nai.

    : Haba yara,

    : Ku koma agwada birni.

    : Sannu ÆŠan Halima na gode ma,

    : ÆŠan Halima na gode,

    : Ka kyauta ma ƙanen Inno.

    : Sha’aibu shuti na gode ma,

    : Sannu Sha’aibu shuti,

    : Mutumin Sani,

    : Wada kai mani,

    : Allah ya kiyaye ka.

     

      Jagora: Kansilan Agwada na gode,

    : Ka taimaki ganga ta.

    : Na tuna Audu,

    : Magajin Agwada sabo,

    : Darzaza Bahagon[7] gulbi,

    : Ka ci gwani dudda jirage nai,

    : Na san ba ka barin bami,

    : Yada kai mani,

    : Ka taimaki gangata.

    : Na so ku haÉ—a min,

    : Waƙa da kiɗin noma.

    : Haba yara ku koma Agwada,

    : Haba yara mu koma agwada.

     

    Jagora: Tun ban je Agwada ba,

    : Ana labarin Agwada birni,x2

    : An ce Agwada naira,

    : Kuma an ce Agwada gero,

    : An ce Agwada dawa,

    : Kuma an ce Agwada maiwa,

    : An ce Agwada ilimi,

    : Kuma an ce Agwada…….

    : Haba yara,

    : Ku koma Agwada birni,x2

    : Daga Maiyama idan han na tashi,

    : Na kama gabas daidai

    : Sai hanyar Agwada,

    : Daga Maiyama idan han na tashi,

    : Na kama gabas daidai

    : Sai hanyar agwada,

    : Haba yara mu koma Agwada,

    : Sun gwada mani,

    : Sun taimaki gangata.

    : To ku tashi mu koma Agwada.

    : Ina É—an mutuwa?

    : Ka kyauta ma ƙanen Inno.

    : Sannu ÆŠanmutuwa[8] Ada,

    : Mai fetur mutunen Sani,

    : To ku tashi,

    : Mu koma Agwada birni.

    : Haba yara,

    :Ku koma Agwada ya fi.



    [1]  Iri É—aya babu garwayi.

    [2]  Naira dubu É—aya yake nufi, ya ari Turanci ne (wato one thousand).

    [3]  DunÆ™ulen fura wanda ba a dama ba.

    [4]  Girgiza yaro don yi masa wasa.

    [5]  Yin kyauta.

    [6]  Bayar da Karin kuÉ—i

    [7]  Babban rafi mai wuyar tsallakewa saboda zurfi da igiyoyin ruwa.

    [8]  Sunansa Adamu ana ce masa ÆŠanmutuwa saboda sana’arsa ta sayar da man fetur saboda yana haddasa gobara.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.