Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

Taƙaitaccen Tarihin Sani Sabulu

Haihuwarsa Da Ƙuruciyarsa

An haifi Sani Sabulu a garin Kanoma da ke cikin ƙaramar hukumar mulki ta Maru ta jahar Zamfara a shekara ta 1952, a wata unguwa da ake kira ‘yar kuka. Sunan mahaifinsa malan Abubakar Kanoma. Mahaifin nasa ya rasu tun yana yaro ƙarami (Kafin ya yi auren fari). A lokacin da yake ƙarami Sani Sabulu ya koyi sana’ar noma da kiyon dabbobi kuma ya zamo mutum mai ƙwazo da juriya. Duk daɗewar da aka yi a gona ba ya nuna gazawarsa. Haka kuma Allah ya bashi fasaha ta yadda duk abin da ya gani zai iya yin irinsa, ko ya kwaikwaye shi. Har wa yau yakan yi farautar namun daji, musanman ma ƙanana irin su kurciya da ɓeraye[1].

Neman ilminsa

Sani Sabulu ya fara karatun Alƙur’ani mai tsarki a hannun mahaifinsa malan Abubakar. Bayan rasuwar mahaifin nasa ne, sai ya koma wajen wani malami da ke nan unguwarsu mai suna malan Hamisu. Daga nan kuma ya koma wata unguwa da ake kira Jauri inda ya cigaba da karatunsa a wajen wani malami mai suna Malam Abdu a nan cikin Kanoma. Bayan ya bar Kanoma ya koma Zariya, ya ci gaba da karatunsa na Addinin Musulunci. A taƙaice dai Sani Sabulu ya sauke Alƙur’ani hizifi sittin, har kuma ya karanci wasu daga cin littattafan fiƙihu kamar su Ƙawa’idi da Ahalari da Ishmawi da Risala.

Wannan ilimi da ya samu, shi yake taimaka masa wajen gudanar da waƙoƙinsa na baka. Don a kodayaushe in zai fara waƙa yakan soma ne da Basmallah tare da ambaton Ubangiji. Ta fuskar ilmin zamani kuwa, Sani Sabulu bai halarci makarantar boko ba, amma ya halarci ajin yaƙi da jahilci a garin Kanoma. Sai dai duk da haka bayanai sun tabbatar da lokacin da Sani yake yawon sa na duniya ya tsinci wasu ‘yan kalmomi na ingilishi. Wannan ma shi ne dalilin da ya sa idan yana waƙa lokaci-lokaci za a ji yana jejjefa ‘yan kalmomin ingilishi a cikin waƙarsa. Kamar inda yake sa kalmar silolin-silolin a wata waƙarsa. Ya aro ne a cikin harshen Ingilishi, wadda ake rubuta ta kamar haka: slowly-slowly, wadda ma’anar ta ke nufin “a hankali a hankali” ko “sannu-sannu”. 

Aure  da iyalinsa

Sani Sabulu ya auri mata guda huɗu ne a rayuwarsa, matan su ne:

i.                    Amina

ii.                 Hajara(Haja)

iii.               Sa’a

iv.               Masa’uda

Ya kuma haifi ‘ya’ya guda shida (6) maza biyu mata huɗu da suka haɗa da:

i.                    Hashimu

ii.                 Jamila

iii.               Nafisatu

iv.               Hindatu

v.                  Balkisu

vi.               Abubakar (Baban gida),

Sai dai ya mutu ya bar matan aure guda biyu wato:

i.                    Hajara

ii.                 Masa’uda.

Waɗannan su ne yawan iyalin Sani Sabulu.

Sana’oinsa

Sani Sabulu bai gudanar da wasu sana’oi da dama ba, baya ga sana’ar gama-gari wato noma, sana’ar da ya fi ba fifiko ita ce makaneza (facin tayoyi), wadda ya koyo daga zariya, kuma ya kawo ta garinsa na haihuwa wato Kanoma. Wannan ya nuna cewa Sani Sabulu bai gaji sana’ar da ya iske mahaifinsa kanta ba, wato dukanci da malanta. Waɗannan su ne sana’oin da Sani Sabulu ya yi a lokacin rayuwar sa.

Baya ga sana’oin gargajiya, Sani ya taɓa yin aikin gwamnati a lokacin da yake zaune a ƙaramar hukumar Koko/Besse da ke jihar kebbi a ƙarƙashin raya al’adun gargajiya na ƙaramar hukumar[2].

Fara waƙarsa

A fagen kiɗa da waƙa, Alhaji Sani Sabulu ɗan haye ne, wato bai gaji kiɗa da waƙa daga iyaye da kakanni ba. Don haka a iya cewa, ya tsiri wannan sana’a ne da rana tsaka. Wannan  zance ya tabbata a cikin ɗaiɗaikun waƙoƙinsa.

Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

Sani Sabulu mutun ne da Allah ya sa ƙauna da sha’awar waƙoƙin baka na Hausa a ƙwaƙwalwarsa, tun lokacin yana yaro ƙanƙane. Waƙoƙin makaɗa irin su Hussaini jikan boka da na Dr. Alhaji Mamman Shata na daga cikin waƙoƙin da suka fi kwanata masa a rai. Saboda kusan duk lokacin da yake gudanar da wani aiki a gona ko a wurin makaneza , za a ji shi yana ta ƙoƙarin rera su. Ta haka ne Sani Sabulu ya Sami gambara ya fara kwaikwayon irin waɗannan waƙoƙi[3].

Bayan Sani Sabulu ya baro zariya ya dawo Kanoma, Allah (S.W.A.) ya jarrabe shi da kamuwa da ciwon kurkunu, Inda ya share watanni  a zaune. To, bayan Allah ya kuɓutar da shi daga cutar ne, sai ya ga ya dace ya shirya wa wannan ciwo waƙa domin ya bayyana irin wahalar da ya sha tare da fito da illolin cutar a fili. Daga nan sai ya ɗauki gambararsa tare da abokinsa mai yi masa mabanci da rikoda da kaset suka fita cikin daji ya shirya waƙarsa tare da  ɗaukar ta kaset

A lokacin da jama’a  suka ji wannan waƙa, sai hankalinsu ya raja’a gare ta. Kuma a dalilin haka ne duk gidan da wata hidima ko sabga ta samu ta aure ko haihuwa, sai su kira Sani Sabulu domin ya shirya masu waƙa[4]

Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

Ana cikin haka ne sai Sani Sabulu ya bar garin Kanoma zuwa garin Koko ƙaramar hukumar Koko/Besse da ke cikin jihar Kebbi. A nan ya sami shiga cikin kungiyar al’adun gargajiya ta ƙaramar hukumar .bayan da suka fahimci fasaha da hikimar da Allah ya yi masa, Sai suka ɗauke shi a matsayin ma’aikaci a gefen wasannin al’adun gargajiya. Duk lokacin da aka sami wani buki, sai su tafi a ƙarƙashin ƙungiyar, suyi raye-raye na gargajiya. Bayan an ƙare raye-raye sai Sani Sabulu ya fito fili domin ya waƙe bikin. Haka kuma a daidai wannan lokaci ne ya waƙe ƙaramar hukumar Koko/Besse[5].

Sani Sabulu a Matsayin makaɗi

Alhaji Sani Sabulu, ya zama cikakakken makaɗI, wanda ya ɗauki kiɗa da waƙa a matsayin sana’a bayan ya bar aikin gwamnati aƙaramar hukumar Koko/Besse. Dagan an sai ya haɗa ƙungiyarsa wadda ta ƙunshi makaɗa da ‘yan ma’abba. Wato dai yana gudanar da san’ar sa ta kiɗa da waƙa ne a ƙungiyance. A daidai wannan lokaci ne ya daina amfani da gambara.

Duk da cewa yana gudanar da kiɗan sa a ƙungiyance, Sani Sabulu shi kaɗai yake aiwatar da waƙarsa ba tare da amshi ba. Sai dai akwai wasu ɗaiɗaikun waƙokin sa ake yi wa amshi kamar waƙar Alhaji Isah Mayana. Wato dai yana  daga cikin rukunin makaɗan jama’a da ke amfani da tsarin nan na kiɗa da waƙa ba tare da amshi ba.

Hausawa na cewa: “Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka”. Sani Sabulu yana da ƙungiya wadda ta ƙunshi  mataimaka ko yara da ke gudanar da ayyuka daban-daban awajen sana’ar sa ta kiɗa da waƙa.

Akwai wasu masu kiɗan kalangu, akwai masu kaɗa ɗan kurkutu kuma akwai sanƙira wato ɗan ma’abba da masu shirya filin wasa, kai harma da direba. A taƙaice dai ga yadda tsarin ƙungiyar tasa take:

i.                    Alhaji Sani SabuluJagora

ii.                 Haruna KokoKaɗa kalangu

iii.               Musa Ɗangarewa“ “

iv.               Mamman Ɗan ƙaddara““

v.                  Shehu Ɗan Ruwan Gora““

vi.               Garba kalangeta““

vii.             Haruna BirgediyaKiɗa kurkutu

viii.          Ado Rano KanoSanƙira

ix.                Ɗan Abu ya yi““

x.                  Shu’aibu Cali““

xi.                Malan Sani““

xii.             Sama’ilaShirya filin wasa

xiii.           Auta Direban mota

Rasuwarsa

A ƙarshe dai Allah ya yi wa Alhaji Sani Sabulu rasuwa a ranar tara ga watan bakwai shekarar dubu biyu da tara 9/7/2009, a sanadiyyar wani hatsarin mota daya haɗu dashi a kan hanyarsa ta dawowa gida daga wajen yawonsa na waƙa.[1]  Sankalawa (1994:9-10).

[2]  Inuwa da wasu (1993:35-36).

[3]  Inuwa da wasu 1993:35-36, Sankalawa 1994:19-20.

[4]  Inuwa da wasu 1993:35-36, Sankalawa 1994:19-20

[5]   Inuwa da wasu: 1993:36.

Post a Comment

0 Comments