Ticker

6/recent/ticker-posts

Malan Shekarau Na Girnace

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Malan Shekarau Na Girnace

Malam Shekarau a garin Girnace yake na yankin Isa ta jihar Sakkwato. Yana aikin gona sosai, hakan ya sa Amali ya yi masa waƙarsa.

 

   G/Waƙa : Koma gona ga haki Malan,

: Masu kai dare gona.

 

Jagora: Malam Shekarau na Girnace,

 ‘Y/Amshi: Malan Shekarau na Girnace,

: Wahala ba ta biyo gidanai ba.

 

Jagora: Niyya Ɗan  Sa’idu,

: Sa ma haki wahala,

   ‘Y/Amshi: Niyya Ɗan  Sa’idu,

: Sa ma haki wahala,

: Mu ga ka ci ƙarhi nai.

 

  Jagora: Ni yau Girnace nikai da kiɗi,

    ‘Y/Amshi: Ni yau Girnace nikai da kiɗin aiki.

: In gano mazan hwama[1].

 

   Jagora: Mamman Girnace nikai da kiɗi.

    ‘Y/Amshi: Ni yau Girnace nikai da kiɗin aiki,

: In gano mazan hwama.

: Koma gona ga haki Malan,

: Masu kai dare gona.

 

    Jagora: Malan ya kira ni,

: Ya yi biyan doki.x2

         ‘Y/Amshi: Malan ya kira ni,

: Ya yi biyan doki.

: Yanzu niy yi zama[2] tai.x2

 

   Jagora: Amma Hushe ta kyauta,

   ‘Y/Amshi: Ta ban sirdi

: Na ji ta yi mai kawu.

 

   Jagora: ‘Yakkware ta kyauta,

    ‘Y/Amshi: Ta ban sirdi.

: Na ji ta yi ma kawu,

   : Koma gona ga haki Malan,

: Masu kai dare gona.

 

    Jagora: Malan Shekarau na Girnace,

     ‘Y/Amshi: Malan Shekarau na Girnace wahala,

: Bata biyo gidanai ba.

: Koma gona ga haki Malan,

: Masu kai dare gona.

  Jagora: Goje duk kag ganai yana,

: Kwan nan-kwan nan,

: Ya zama mahelheci,

: Ya zan sha-ka bani,

: Ya zama tunhwaya, 

   ‘Y/Amshi: Ya zama tunhwaya[3] ,

: Ban iya yi mai hira.

 

   Jagora: Ƙato duk kag ga yana,

: Yawon iska,

: Ya zama duman rani,

: Wannan ya ɓakita,

: Ya zama tunhwaya,

: Ya zama duman rani.

    ‘Y/Amshi: Ya zama duman rani,

: Koma gona ga haki Malan,

: Masu kai dare gona.

 

   Jagora: Niyya Ɗan Sa’idu,

: Sa ma haki wahala,x2

   ‘Y/Amshi: Niyya Ɗsn Sa’idu,

: Sa ma haki wahala,

: Mu ga ka ci ƙarhinai.x2

: Koma gona ga haki Malan,

: Masu kai dare gona.



[1]  Manyan manoma.

[2]  Sukuwa da doki don nuna gwaninta.

[3]  Ciko, wato idan wani mazubi bai cika ba sai a tunhwaye.

Post a Comment

0 Comments