Ticker

6/recent/ticker-posts

Garba Dauran (Ta farko)

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Garba Dauran (Ta farko)

Garba Dauran Shahararren manomi ne a yankin Zurmi ta jihar Zamfara. Ma’aikacin gwamnati ne wanda ya shugabanci ƙaramar hukumar zurmi a 2011 har zuwa 2015. Yana da manya-manyan gonaki kuma mai arzikin noma ne, hakan ya sa mawaƙa suke yi masa waƙa daga cikinsu har da Amali  Sububu.

 

     G/Waƙa : Jijjihi[1] yakai daji,

: Baya wargi,

  : Kodayaushe shi dai bai,

: San sake ba,

: In yi mai kiɗin aiki,

: Garba Dauran.

 

 Jagora: Mun kwana munka yo sallah,

: Munka dawo,

  : Amali na yi hul tanki,

: Tun da sahe,

  : Ni dai ina ta ɗora giya,

: Babu dama,

  : Mun zo Arewa mun yi kwana,

  : Munka kwan nan.

‘Y/Amshi: Jijjihi yakai daji,

: Baya wargi,

  : Kodayaushe shi dai bai,

: San sake ba,

: In yi mai kiɗin aiki,

: Garba Dauran.

 

Jagora: Mun kwana munka yo sallah,

: Munka dawo,

  : Amali niy yi hul tanki,

: Tun da sahe,

  : Ni dai ina ta jehwa giya,

: Babu dama,

  : Mun yo Arewa zamu kwana,

: Munka kwana,

  : Ran nan ana cikin la’asar,

: Munka dawo.

 

‘Y/Amshi: Jijjihi yakai daji,

: Baya wargi,

  : Kodayaushe shi dai bai,

: San sake ba,

: In yi mai kiɗin aiki,

: Garba Dauran.



[1]  Sammako tun gari bai waye ba.

Post a Comment

0 Comments