Ticker

6/recent/ticker-posts

Za Mu Iya Aurar Da 'Yarmu Ga Ɗan Shi'a?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ina da 'yar'uwa sama da shekara goma tana soyayya da ɗan shi'a, anyi anyi ta rabu dashi taƙi, har ta shiga shi'ar, iyayenta sunƙi aura mata shi, yanzu an samu wasu adangi 'yan bidi'a zasu daura musu aure, shin ya halatta muje bikin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Idan Allah ya datar da Mutum ya shiryar da shi da bin hanyar Ahlussunnah wal-jama'a, to dole ya san abubuwan da zasu raba shi da abin da Ahulussunnah wal-jama'a suke akai don nesantar su, ya kuma san Abin da 'yan shi'a suke akai na aƙidu mugwaye da tafarki.

Asalai da 'yan shi'a suka saɓawa ahulussunnah akansu suna da yawa daka cikinsu akwai:-.

'yan shi'a suna ƙudurce jirkitar alƙur'ani badai-dai yake ba, suna ƙudurce limamansu basa Saɓo, sun kafirta sahabbai baki ɗaya sai 'yan kaɗan da suka bari ba su kafirta ba, suna girmama Ƙabur-bura, da raya su, suna neman agajin mamacin dake cikin ƙabari da roƙonsa biyan wata buƙata, a mai-makon Allah, duk Wannan ya samo asali saboda baƙar ƙiyayya da hassada da suke da ita a kan ahlusunnah Wal-jama'a, da kafirta su da sukayi, ta yaya zaka Aurar da 'yarka ga wanda wannan shi ne aƙidarsa, ta yaya kake tunani zai samu nasara arayuwa tare da tattaruwar wannan tufka da War-wara da yake da ita acikin addini? ta yaya zai tarbiyanci 'ya'ya?, a kan tauhudi zai rainesu ko a kan shirka da ba ta da maguzanci? shin kanajin Zai koya musu son sahabbai, ko ƙinsu zai koya musu?, shin zai koya musu Tsarkakuwar limamansu goma sha biyu, ko zai koyar dasu mantuwa da kus-kure yana iya faruwa dasu?, da sauran Abubuwa masu yawa na tufka da War-wara.

Indai Mutum ɗan shi'ane ko an daura masa Aure da yarinya wannan auren bataccene, bai halatta Mace ta Aureshi ba, domin waɗannan aƙidun suna kishiyantar addinin musulunci ne, Allah madaukakin Sarki ya ce a suratul Baƙara aya ta 221:

وَلَا تَنْكِحُوا الْمُشْرِكَاتِ حَتَّىٰ يُؤْمِنَّ ۚ وَلَأَمَةٌ مُؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ ۗ وَلَا تُنْكِحُوا الْمُشْرِكِينَ حَتَّىٰ يُؤْمِنُوا ۚ وَلَعَبْدٌ مُؤْمِنٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكٍ وَلَوْ أَعْجَبَكُمْ ۗ أُولَٰئِكَ يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ ۖ وَاللَّهُ يَدْعُو إِلَى الْجَنَّةِ وَالْمَغْفِرَةِ بِإِذْنِهِ ۖ وَيُبَيِّنُ آيَاتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

FASSARA:

Kuma kada ku auri mãtã mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũmina ita ce mafi alheri daga ɗiya kãfira, kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alheri daga ɗa mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa.

An tambayi Shaikul Islam ibnu taimiyyah a kan shin ya halatta mace ta auri ɗan shi'a ko na miji ya Auri 'yar shi'a?.

Ya Amsa da: 'yan shi'a masoya son zuciyane da bidi'a da ɓata, bai kamata musulmi ya Aurar da 'yarsa ko wacce yake da walicci akanta ga ɗan shi'a ba.

Idan ita ma 'yar shi'ace, aure yayi, idan ana fatan zata tuba, idan ita macen ce 'yar shi'a namijin ba ɗan shi'a ba ne, kuma ba'a tsammanin zata tuba, barin Aurenta shi ne yafi, don kada ta ɓata masa 'ya'yansa.

Maj-mu'u fatawa (32/61).

Kaga A nan shaikul islam ya hana auren 'yar shi'a, duk da Aure yana sanya miji yayi tasiri a kan matarsa, ya halatta auren 'yar shi'a idan ana fatan tuban ta..

idan Mutum yaga aurenta zaisa ya tsayar da ita a kan hanyar gaskiya.

Amma Idan Macece Ɗan shi'a ya nemi Aurenta kai tsaye haramunne a daura musu aure, idan An daura auren baiyi ba.

Ta kowacce hali babu wata hujja da uba zai ƙyale wasu tsoffi 'yan bidi'a yanaji yana gani su aurar wa da ɗan shi'a 'yarsa, wannan ya nuna shikansa bai san me yake yi ba, ranar ƙiyama kai uba kai Allah zaiwa tambaya dangane da kiwon 'ya'yanka da Allah ya baka.

ba dai-dai ba ne iyaye maza sudunga ƙyale Al'amarin auren 'ya'yansu a hannun kakanninsu ko iyayensu koda kuwa su ba su aminta da aƙida ko halaye na wannan da yake neman 'ya'yansu ba.

Uba shike da haƙƙin Aurar da 'yarsa ga mutumin daya aminta da halayyarsa da Addininsa da Aƙidarsa.

Wajibine a kan Uba ya tashi tsaye yayi bincke mai ƙarfi a kan duk wanda yazo neman Auren 'yarsa.

Idan ya tabbatar bashi da aƙida ko halayya mai kyau, to shi ne yake da cikakken iko da hurumin Auren da 'yarsa, in yaga mutum bashi da aƙida mai kyau, to karya sake wasu tsoffi su yi masa dole, ya tsaya tsayin daka ko sama da Ƙasa zata haɗe karya Aurar da 'yarsa ga mutumin banza mushiriki.

Yanzu ba Maganar zuwa Daurin Aure ba, ko an daura ma Auren baiyi ba.

Dolene a kan uban wannan yarinya ya tsaya yaga 'yarsa ba ta Auri wannan zindiƙin ba, duk irin rikicin da za ayi saidai ayi 'yarkace kai Allah zai tambaya a kan Amanarta daya damƙa ahannunka.

Kada Ku sake ayi wannan Auren iskanci da fasadi mai yawa dake cikinsa.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments