Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mijin Da Ya Ƙaurace Wa Matarsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne hukuncin mai gidan da ya daina yiwa matarsa magana, dan ya ba ta damar tafiya wani gari ba ta dawo ba tayi zamanta, saboda mai gidan ba mazauni ba ne, shi yasa ba ta bin umarninsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Allah ya shar'anta Aure saboda da hukunce hukunce masu yawa, daka cikinsu akwai samun nutsuwa da samun kwanciyar hankali tsakanin ma'aurata dansu tsayu wajan tarbiyyar 'ya'yansu acikin kwanciyar rai.

Allah ya shar'anta jumillar wasu haƙƙoƙi daka cikin haƙƙoƙi wajibai ga kowa cikin ma'aurata, dansu zama kadargo na tsare wannan alaƙa wacce Allah ya ambaceta da Alƙawari mai ƙarfi acikin aya ta (128) cikin Suratul Baƙara.

Bai Halatta Namiji ya ƙauracewa matarsa sai idan ta zama fandararriya, wacce ba ta kiyaye haƙƙoƙinsa, ya halatta ya ƙaurace mata awannan lokacin, harsai ta dawo ta gyara halinta, Kamar yanda Allah madaukakin Sarki ya fada acikin aya ta (34) cikin Suratul Nisa'i.

الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ وَبِمَا أَنْفَقُوا مِنْ أَمْوَالِهِمْ ۚ فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ حَافِظَاتٌ لِلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ اللَّهُ ۚ وَاللَّاتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَاهْجُرُوهُنَّ فِي الْمَضَاجِعِ وَاضْرِبُوهُنَّ ۖ فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيًّا كَبِيرًا

FASSARA:

Maza mãsu tsayuwa ne a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihan mãtã mãsu ɗã´a ne, mãsu tsarewa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa´annan kuma, idan sun yi muku ɗa´a, to, kada ku nemi wata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.

Idan Miji ya Ƙauracewa matarsa Saboda laifin datayi masa wanda shari'a ta halasta masa ya ƙaurace mata, to ita haramunne tace ita ma zata biye masa ta ƙaurace masa, domin yin hakan ƙara kangarewace wanda yake haramun.

Amma Idan ya ƙaurace mata ba tare da wani Abu na shari'a daya bashi dama ba, tana da damar ita ma ta ƙaurace masa, Kamar yanda Allah madaukakin Sarki yafada acikin aya ta (126) cikin Suratul Nahli.

Amma Bazata hana shi haƙƙinsa na jima'i dajin daɗi da itaba.

Nasiharmu ga Ma'aurata ita ce: Ku nisanci dukkan Abin da zai haifar da sakwar-kwacewar alaƙa tsakaninku, kudunga gaggawa zuwa ga Abin da zai gyara tsakaninku Kamar yanda Allah yafada a aya ta (134) acikin Suratul Ãli Imrãan.

الَّذِينَ يُنْفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ

FASSARA:

Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyewar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.

Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: Inayi muku wasici a kan mata da Alkhairi, domin An halicci mace daka karkataccen ƙashin haƙar-ƙari, abin da yafi komai karkacewa a haƙar-ƙari shi ne saman sa, idan kace saika miƙar dashi zaka karya shi, idan ka ƙyaleshi haka zai ta zama akar-kace, Inayi muku wasici ga mata da Alkhairi.

Bukhari (3084) Muslim (2671).

Ya kamata Mu sani Allah ya halatta ƙauracewa macene danta gyara halayenta da dabi'unta, badan acutar da ita ba, kodan taƙara kangarewa ba.

Idan kaga ƙauracewar bazai gyara taba, sai kayi wani abun da zai gyarata wanda ba ƙauracewar ba, saika kame daka ƙauracewar, kasami wata hanyar ta gyara mata halayenta, daka ciki akwai fahimtar juna tahanyar bayyana mata halayenta ƙarara da tattaunawa da ita a kan Al'amura bisa Gaskiya da Adalci da ƙas-ƙan da kai, wajibine ka koma ga gaskiya idan ya tabbata kaine kake zaluntar ta, wannan shi ne abin da zaifi tabbatar da alaƙarku da dawwamarta, idan duk wadannan hanyoyin kabi ba'ayi nasara wajan magance fandarewar matar ba, Saika Kira wasu daka cikin dangin iyayenta da iyayenka, dansu war-ware matsalar, su yi muku hukunci acikinta, kamar yanda Allah madaukakin Sarki ya fada acikin aya ta (35) cikin Suratul Nisa'i.

وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوا حَكَمًا مِنْ أَهْلِهِ وَحَكَمًا مِنْ أَهْلِهَا إِنْ يُرِيدَا إِصْلَاحًا يُوَفِّقِ اللَّهُ بَيْنَهُمَا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا

FASSARA:

Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma´auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.

Amma Idan ba kangarewa matarka tayi ba, bai halatta ka ƙaurace mata ba saboda Abubuwa guda biyu.

1- Wajibine mijine yadunga yiwa matarsa afuwa. yayi jima'i da ita gwar-gwadon buƙatar ta da ikonsa. Kamar yanda shaikul Islam ibnu Taimiyyah Allah yajiƙansa da rahama yafada acikin Maj-mu'u fatawa dinsa, (32" 271).

2- Wanda yaƙi saduwa da matarsa wacce ba kangararriya ba ce, ya shiga ƙar-ƙashin hukuncin bawa za a umarceshi ya sadu da ita koya saketa, in yaƙi Alƙali ya sake ta. Kamar yanda Malaman Lajnatul da'imah suka bayyana (20/443).

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments