Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Harama Daga Tan'im (Masallacin Nana A'isha)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam. Mun kammala aikin Hajji, kuma har yanzu muna Makkah, mun shiga sabon wata, shin zan iya ƙara yin Umara daga Tan'im? Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Za ka iya yin sabuwar Umara, amma sai ka je Miƙati ka dauƙo a zance mafi inganci, kamar Zul-hulaifah, miƙatin mutanen Madina, ko Yalamlam, miƙatin mutanen Yaman.

Tan'im (Masallacin Nana A'isha) ba ya cikin miƙatai guda huɗu da Annabi ya ƙayyade, wannan yasa irin ka da yayi Hajji da Umara ba zai ɗauko Hajji daga wurin ba.

Duk da cewa wasu Malaman sun halatta ɗauko Umara daga Tan'im, saboda Hadisin Bukhari lokacin da Nana A'isha tayi haila bayan ta yi niyyar Tamattu'i, Annabi ya umarci ɗan'uwanta Abdurrahman ya kai ta wajen Haramin Makkah ta ɗauko Umara saboda nuna damuwarta da tayi na rashin samun Umara keɓaɓɓiya, sai dai ba'a samu Sahabbai suna ɗauko harama daga wurin ba, haka nan magabata nagari. Hakan sai ya nuna hukuncin ya keɓanta da ita da masu lalura irin tata.

Alhajin da bai samu maimaita Umara ba daga miƙati zai iya shagaltuwa da Ɗawafi da addu'o'in neman gafara da Fatahi a wajan Allah.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments