Ticker

6/recent/ticker-posts

Yaushe Ne Lokacin Yanka Layya?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam wani lokaci ya kamata a fara yanka layya kuma wani lokaci yake karewa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Lokacin fara yanka layya yana farawa bayan Sallar idin babbar Sallar, yana ƙarewa bayan faduwar ranar sha Uku ga Watan zhul-hijjah.

Ma'ana kwanakin yanka layya huɗu ne, Ranar babbar Sallah da kwana uku bayanta.

Abin da yafi falala shi ne mutum yayi Saurin yanka dabbar layyarsa bayan Sakkowa daka Idi, kamar yanda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yake Aikatawa, sannan Ranar Sallah ya Zama Abin da zaka fara ci shi ne naman layyarka.

Imamu Ahmad ya ruwaito hadisi (22475) daka Buraidah Allah yaƙara yarda dashi ya ce: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam baya fita Sallar idin ƙaramar Sallah harsai yaci abunci, baya cin Abunci A babbar Sallah harsai ya dawo daka Idi, sai yaci daka naman layyar sa.

Zaila'i ya ciro wannan hadisin acikin Nasburraya (2/221) daka Ibnu ƙaddaan ya ingantashi.

Ibnul Ƙayyeem acikin zhadul ma'adi ya ce: Aliyu ya ce: Ranar yanka, shi ne ranar sallah, da kwana uku bayanta.

Shi ne mazhabar Imamu Ahlul basra, hasanul basary, da limamin Mutanen Makkah, Ada'a bin Abiy rabah, da limamin mutanen Shaam Auza'iy, da Limamin Malaman fiƙhun hadisi Shafi'i Allah yajiƙansu.

Ibnu munzir ya zaɓi wannan zancen, Saboda kwanaki ukun sun keɓantu da kasancewarsu, Kwana a mina, da jifan jamrah, da ayyamul tashreeƙ, haramunne a azumtarsu, 'yan'uwane wajan hukunci, ta yaya za a rabasu wajan halaccin yanka ba tare da nassi ba, ba kuma tare da ijma'i ba..

An samu Ruwaya ta fuska biyu kowacce ta saɓa da dayar, Sashinsu yana Ƙarfafar sashi daka Annani Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Dukkan ranar mina ranar soke hadayace, dukkan kwanakin tashreeƙ ranakun yankane.

Albani ya ingantashi acikin Sil-sila saheeha (2476).

Yankawa da an dawo idi shi ne yafi falala, sannan kowacce rana tafi falala a kan maibi mata.

Amma Idan Ka manta, ko dabbar ka ta ɓata baka gantaba sai bayan waɗannan kawanaki, ko ka wakilta wani ya yanka maka ya Manta babu laifi ka yanka bayan waɗannan kwanaki.

Malaman Lajnatul Da'imah sukace: Kwanakin yanka hadaya ta tamattu'i da Ƙirani da layya kwana huɗu ne, lokacin yanka yana ƙarewa bayan faduwar rana ta huɗu da yin idi.

Fatawa lajnah (11/406).

Wallahu A'alamu.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments