Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Daga Cikin Hukunce-Hukuncen Da Suka Shafi Ranar Idi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum,

Malam ina so sanin hukunce-hukuncen idi

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam. Idi yana da hukunce-hukunce da yawa ga wasu saga ciki:

1. Azumtar ranar idi – ya haramta a azumci ranakun idi guda biyu, saboda hadisin Abu-sa'id Al-kudry, -Allah ya yarda da shi - cewa: "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana azumtar ranaku biyu – wato ranar karamar sallah da ranar babbar sallah" Muslim ya rawaito

2. Siffar sallar idi- An karbo daga Abu-sa'id -Allah ya yarda da shi – cewa: "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana fita ranar idin karamar sallah da babbar sallah zuwa filin idi, idan ya fita yana farawa da sallah" Bukari ne ya rawaito

Ana yin ta ne raka'o'i biyu, za a yi kabbara bakwai a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma sai ayi kabbara shida. Abu-dawud

Idan mamu ya riski limaminsa a tsakiyar kabbarori, to zai yi kabbarar harama ne ya bi shi, ba zai rama abin da kubce masa ba na kabbarori, saboda sunnoni ne ba wajibai ba.

Dr. Jamilu Zarewa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments