Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Auri Amare Biyu A Rana Ɗaya, Ya Ya Kamata Na Yi Wajen Tarewa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam mutum ne ya auri mata biyu (sangaya) rana guda, to dakin wacce zai fara shiga? Na gode, Allah ya kara wa malam imani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To dan’uwa wasu daga cikin malamai sun karhanta auran mata biyu a yini ɗaya, saboda hakan zai kawo matsala wajen ba wa matan hakkinsu na kwana, saboda duk wacce aka fara da ita, to dayar za ta cutu, sai dai idan hakan ta faru, to zai fara ne da wacce ta fara shigowa gidan, in kuma sun shigo tare ne sai ya yi musu kuri’a.

Don neman karin bayani duba: Al-kafy Na Ibnu Khudaamah shafi na: 981.

Allah ne ma fi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers


Post a Comment

0 Comments