Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Halatta Na Bawa Kirista Naman Layya?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun alaikum, Malam zan iya bawa makocina kirista naman layya ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Ya halatta a ba wa kafiri naman layya, mutukar babu yaki tsakaninsa da Musulmai, Allah Yana cewa a suratul Mumtahanah aya ta (8): "Allah Ba Ya hanaku kyautatawa kafiran da ba su yake ku ba, ba su Kuma fitar da ku daga gidajanku ba"

Ibnu Khudama Yana cewa: "Layya sadaka ce, don haka ya halatta a bawa kafiri kamar ragowar sadakoki na nafila" Almugni 9/450.

Annabi Yana cewa: "Mala'ika Jibrilu bai gushe yana min wasici da makoci ba, har sai da na zaci zai ce akwai gado tsakanin makoci da makoci".

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments