Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saurayin Da Yake Taɓa Jikin Budurwarsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam Khamis. da fatan anyi sallah lafiya. Mene ne hukuncin saurayin da yake taɓa jikin budurwarsa yana shafa mata nono da sunan Soyayya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

To wannan ba soyayyah ba ce kiyayyah ce, tsantsar soyayyah tana cikin yin ladabi ga Allah da Manzonsa amma saurayi ya taɓa jikin budurwarsa wannan ai kiyayyah ce yake nuna mata ba soyayyah ba, wannan abin da suke aikatawa mummuna ce, Tun da Allah ya haramta taɓa jikin matar da baka aura ba, kuma kofa ce da za ta kai zuwa zina.

Allah maɗaukakin sarki idan ya haramta wani abu yakan haramta dukkan wata hanya komai kankantarta da zata kai zuwa ga aikata wannan abun. Saninmu ne taɓa ko shafar jikin mace babbar hanya ce wadda ke motsar da sha’awa zuwa ga aikata zina.

Duk macen da ta bada kanta wa wani dan iska mayaudari wanda baya sonta baya son rayuwarta da tarihinta da sunan wai yana sonki ko kuma kunyi alkawarin aure wallahi duk yaudara ce, duk wanda za ki masa haka kina tunanin zai aminta cewa idan wani yazo gunki ba za ki bashi irin damar da kika bashi ba? Kiyi tunani da kyau yake ‘yar uwa! ba wani sonki da yake kawai wani abu ya keso ya cimma akanki na mummunan aiki ya ɓata ki dajin kunyar duniya data lahira. Ki sani da zarar ya cimma mugun burinsa akanki shi ne zaifi kowa kyamarki da gudunki, koba kuɗi bazai yarda ya aure ki ba.

Hadisi ya tabbata wanda Manzon Allah ya ce: Abuga Narkakkiyar kusar wuta ta bakin karfe a kan ɗayanku shi yafi masa alkhairi a kan ya shafi jikin macen da ba ta hallata agareshi ba. Albany ya ce hadisine ingantacce acikin sahihul jami’ul kabeer (5045).

kinji fa da ace yau gashi mutum ya taɓa matar da ba tashi ba yafi masa sauki ayi masa wancan aika-aikan kinga kuwa abin babba ne! Haka kuma babu makawa yayin wannan shafe-shafen dole ayi zinar ido, zinar kunne, zinar harshe da kuma zinar kafa.

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Abu Hurayrah (Allah ya yarda dashi) Annabi ya ce: ”Allah yana rubutawa ɗan Adam kasonsa na zina, zai riski wannan kason babu makawa, zinar ido ita ce kallo, zinar kunne saurara, zinar harshe zance, zinar kafa tafiya, zuciya tayi buri tayi sha’awa, farji shi zai yarda ko ya karyata”

Waɗannan hadisan kaɗai ya isa ya zama tsawa da firgitarwa ga samari da kuma ‘yan matan da ake yaudara da sunan ana sonku, ya isa kuji tsoron Allah ku tuba tun kafin lokaci ya kure muku, ku lazumci yiwa Allah biyayya cikin abin da ya haramta na dokokinsa, na daga abin da shafar mace yake haifarwa wanda yake kaiwa zuwa ga fitintunu da alfasha kala-kala.

lallai tsantsar soyayyah tana cikin bin tafarkin Allah da kuma bin Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Allah yasa mudace.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments