Ticker

6/recent/ticker-posts

Wata Rana (002)

Allah ya jiƙan magabatanmu, amin. Wata rana wani mutum dake zaune a garin Tsafe a farko farkon mulkin Marigayi Yandoton Tsafe Aliyu II ya kai koke wajen Yandoto cewa yayarsa /yarsa wadda ya baiwa riƙon wani ɗansa ta hana ya sanya yaron/ɗan nasa a Makarantar Boko (saboda ita yayar tasa Malamar Addinin Musulunci ce mai ƙyamar karatun boko).

Da yamma sai Marigayi Yandoto ya aika aka kira ta. Ta taho fada bayan ta yi gaisuwa sai ya ce mata "Ina cikin wata fargaba ce akan yaron nan dake wajen ki ɗan Ƙanen ki wane, domin ke san yanzu bamu da iko sosai Turawa sun ƙwace muna iko mai dama sun mayar akan jami'an gwamnati. An aiko mani da takarda ne cewa mu ba da wannan yaro zuwa Makarantar Mishau(domin a lokacin akwai Mission School da Turawa suka buɗa a nan Tsafe), to ni ban ma san yadda za ayi wannan lamari ba". Hankali Modibbo ya tashi sosai ta ce wa Yandoto "Ikon Allah, to su ko ina laihin su ce wannan makaranta ta gari(Township Primary School ta Tsafe a lokacin)? Amma ace ta Mishau, haba dai Ranka ya daɗe". Da Yandoto ya ga ya samu sa'arta sai ya ce " To Modibbo bari mu gani ko zasu amince a saka shi wannan ta gari ɗin a maimakon tasu ta Mishau". Modibbo tace to don Allah dai Ranka ya daɗe a yi muna ƙoƙari a ga ko zasu amince sai a saka shi wannan ta gari ɗin. Haka suka yi bankwana tana ta nanatawa Yandoto, ta hakan ne wannan yaro ya shiga makarantar boko har sai da ya zamo babban jami'in Gwamnati har ya zuwa lokacin ritayarsa, ya na nan raye a halin yanzu.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com

Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments