Ticker

6/recent/ticker-posts

Barka Da Zuwa Nijeriya - Barkwanci

 1. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da ake kiran Miji da Baby Jariri kuma a kira shi Daddy 🙄

2. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da biki dole sai ranar Asabar ko ranar Lahadi 🙄

3. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da take bawa wasu kasashen tallafin wutar lantarki yayinda ita kuma ta kasa tsayar da Wutar a Kasar ta 🙄

4. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da Makullan Mota da wayar IPhone ba a saka su a Aljihu saboda Burga 🙄

5. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da cikin Sauki da kwanciyar Hankali ake tara dubunnan Naira domin zaman makokinka amma ba za a taba baka jari ba lokacin da kake a Raye 🙄

6. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da kana bude Firji maimakon kaga tarin ababen sha dana tande tande saidai ka ga tarin Zogale da yakuwa 🙄

7. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da zaka siyo Kare sannan ka sanya musu suna Tiger 🙄

8. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da mai Aure zaka ji yana fadin Budurwarsa na cin Amanarsa 🙄

9. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da yan damfara suke da gobe mai kyau fiye da wanda ya kammala karatu 🙄

10. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da masu Aski suke manna hoton Askin da ba zasu iya irinsa ba 🙄

11. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da Magani 1 yake warkar da cututtuka sama da 50 🙄

12. Barka da zuwa Nijeriya Kasar da Matasa suke Rina gashinsu zuwa Fari tsoffi kuma su Rina nasu zuwa Baki 🙄

13Barka Da zuwa Nijeriya kasar da budurwa zata iya hakuri da talauchin babanta Amma ba ta iya jurewa gidan mijinta😂😂😂

NIJERIYA KASARKU TA GADO 😂😂😂

Barka Da Zuwa Nijeriya - Barkwanci

Post a Comment

0 Comments