Ticker

6/recent/ticker-posts

Wata Rana (001)

Wata rana a farko farkon shekarun 1980s, muna zaune a garkar mai garinmu (Birnin Magaji dake cikin Jihar Zamfara a halin yanzu) bayan an kammala Sallar Isha'i sai ga wata mata tazo da ƙorafi game da mijinta a wajen mai garin namu(Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman a lokacin ya na matsayin Dagaci. Ya yi sarauta daga shekarar 1945 zuwa rasuwarsa a watan Oktoban shekarar 2005) cewa ta na son a raba aurensu. Ɗan Ali ya dalla mata tocilan ya tambaye ta wane ne mijin nata, ta gaya masa, ya sake tambayar ta me ya sa ta ke neman a raba auren nasu, ta ce ta dai gaji ba ta iyawa.

Nan take ya aika aka zo da mijin da kuma iyayen wannan matar a gabansa. Ya sake tambayar ta bahasi, sai ta gaya masa cewa suna zaune tare da mijinta ne a cikin gidansu(mijin) na gado, kenan akwai magidanta da iyalansu a ciki da yawa. Ya ce ya na barin ki da yunwa ko tsumma ko kwaɗayi ko rashin zamantakewar aure ne? Ta ce ko alama, ya ce to wace irin matsala ce mai nauyi haka har kike neman rabuwa dashi? Ta ce duk cikin mazauna wannan gida da suke a ciki ita ce kurum ke tu'ammali da Tsabar Dawa wajen yin fura da kuma Tuwo saboda haka ta gaji da wannan abin kunya.

Ɗan Ali ya ce madalla, ya aika a cikin gidansa a zo mashi da fura, aka shiga aka karɓo fura a cikin kwano aka kawo masa. Ya shanye kusan rabin kwanon furar nan, sannan ya ajiye kwanon a ƙasa, ya dalla tocilan a cikin kwanon ya ce tun da matar tana tu'ammali da tsabar dawa za ta iya gane fura idan ta dawa ce, ta ce masa haƙiƙa, ya ce to ta duba wannan furar me ce? Ta ce  furar dawa ce, ya ce mata da Ɗan Ali da iyayenki wa ne ne ya fi girma a garin nan? Ta ce Ɗan Ali ne mafi girma, ya ce ke lura furar dawa ya ke sha a gidansa ballantana ke ki ce baki son tu'ammali da dawa ko? Ta ce eh Allah ya baka nasara, ya ce to ba za raba ki da mijin ki kan wannan dalili ba, na mayar dake ɗakinki kuma daga yau kada in sake jin irin wannan magana. Ya juya wajen iyayenta ya ce masu ku dinga tsawata ma yaranku domin kaucewa irin waɗan nan ƙananan maganganu. Allah ya yi maku albarka, miji da iyayen matar suka yi godiya suka tashi.

Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com

Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments