Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙeƙeniya Tsakanin Muhammad Muktar (Maisugar) Da Aminu Sani Uba (Abu Isah Asshankidy)

Muhammad

1. Shin zaku barni na shaƙata ne kokwa dai?

Sai nayi ƙwaƙuduba gami da hatsaniya.

 

2. Ni ne kaɗai mai zuge tsinke kai guda,

Ni ke zama sarki a waƙeƙeniya.

 

3. Ni ne nake kutufo da alƙalami idan-

 Aka ambace ni sukanyi watsin watsiya.

 

4. Ni ne kaɗai kayin dubu ɗaya ba jira,

Ni ne nake wanke shirinsu gaba ɗaya.

 

5. Ni ɗai ka furta guda tazam tamkar dubu,

Su sunyi-sunyi su tazaga kan ya ƙiya.

 

6. Sun ambace ni suna ganin dai-dai dasu,

Sai aljaninsu yace da su "ni ban iya" .

 

7. Suka zo gare ni suna ta neman lamuni,

Har zabiyar ga tana ta neman yafiya.

 

8. Wai ni ina suke ne mawaƙan kokwa dai?

Sun lallaɓa sun zagaye ta mazagaya.

 

9. Yau dai ina tsaye kyam gabanku saman dubu,

Zan ɗauki bulala kamar mai zaniya.

 

10. Duk wanda zai yi amo saman mai yin amo,

To babu shakka zai ji saukar tsamiya.

 

 

 

Aminu(Abu Isah Asshankidy)

11. Kai Dan tsaya yaro staya nan don kaji,

Domin a nan da Akwai gwaninka a ƙafiya.

 

12.    Ni ne idan har nayyi baiti na guda,

To in nayo jama'ar garin mu ya zagaya.

 

13. Duka basu gane mai nace a cikin batun,

Domin kwa baitin ya zamo ya Wahainiya.

 

14. Sai sui zaton na ce kaza Amma kwa ni,

Maganar da nai nasan akwaita akwai wuya.

 

15. Sai dai su dawo nan wuri na don suji,

Domin kwa Hausar tasu Sam ba lafiya.

 

16. Ni ne mawaƙa ke jira domin su ji,

Ni ne kasumi na ka neman yafiya.

 

17. Domin kwa yasan in na ɗau Alƙallami,

Kashin sa ya bushe da zar na dulmiya.

 

18. Ni ne sarakai ke Kira domin na yo.

Waƙe gare su ya zam karaɗe Duniya.

 

19. In har na ce yau za na yo alfahhari,

To ba batun wani ma ya buɗe Idaniya.

 

20. Domin kwa komai zai faɗa bai kai ya ni.

Domin kwa manzo ne fa ni gun ƙafiya.

 

 

 

 

 

 

 

Muhammad(Maisugar)

21. Kai dakata kaji nifa na ja sansani,

Na kutsa kai a cikin taɓo da cikin ƙaya.

 

22. Na danna kai na inda ma baka zato,

Na shallake nisan dare sarƙaƙiya.

 

23. Na taka tsauni na bi dukka kwazazzaɓai,

Na taka rami kan taɗai da ƙarangiya.

 

24. Na samu taron sha'ira daga nesa ma,

Suka ce dani "mun barka mun san ka iya".

 

25. Ballantana sauro da ke bin lunguna,

Don tsince-tsince da rana wai shi jan wuya.

 

26. Ni ne karen bana na wuce zomon bana,

Koda cikin kogi na kan saka rariya.

 

27. Zan so ku tambayi ƴan'uwa na saman dare,

Wannan dake tafiya da sanyin safiya.

 

28. Ko ramukan da suke wuyar tsotse ruwa,

Na sha ruwa daga zabako da maɗaciya.

 

29. Na maida alƙalami dubu harafi guda,

Ni ne ka sharen ƙulafutan su da tsintsiya.

 

30. Waƙa gida na ne a barni na wataya,

Ni ne kaɗai sarkin ta ko da Tsiya-tsiya.

 

 

 

 

 

 

 

Aminu(Abu Isah Asshankidy)

31. Kai wanne zance ne kake ba kan gado?,

Daga jinsa ya fi kama ace Tatsuniya.

 

32. Wane mutum wane mutum kowa yake,

Ya iso garen koda gidansu da Zabiya.

 

33. Ni ne nake waƙe cikin sa a guda,

Haka zata zo wal-wal kamar dai Walkiya.

 

34. In sha'irai suka jita sai sun kwaikwaya,

Yaro ka zauna kar ka zam mai tankiya.

 

35. Tun can fagen Waƙa fa ni na gagara,

Wasu sha'irai suka so suyi min Kurciya.

 

36. Sai dai fa kash! ai sun riga sun makkara,

Bokansu ya ce tuntuni ni na iya.

 

37. Sui haƙƙuri domin kwa ni ne Kan gaba,

Ba Mai wuce ni idan ina nan Duniya.

 

38. Suka zo garen suka durkusa suka mika Kai,

Don na zamo can Kan gaba lamba Ɗaya.

 

39. Kar dai ku manta tun a can na fada muku,

Ni akka baiwa ƙafiya ko kun ƙiya.

 

40. Ban San yabon Kai na a bainar jamm'a,

Domin hakan shi ne ka tada hatsaniya.

 

Muhammad(Maisugar)

41. Wai kai ina ka fice da har aka san ka ma?

Zai dai fi kyau ka tsaya gida ka ci taliya.

 

42. Ni ne ka yin sauti ya farfasa ganguna,

Ni ne ka yin magana a tsaida hatsaniya.

 

43. Harni ka ke tankawa in nai baituka,

Lallai fa yaron nan kana da ƙiriniya.

 

44. Yau zan kaɗe ƙurar da ke ruɗa ta ka,

Na sanar da kai bam-ban zuma da maɗaciya.

 

45. Don ni sahara koguna nan ne gida,

Yara da mata sunka jurar kwalliya.

 

46.   Hular sarautar ƙafiya na ƙaƙaba,

Na sa fara na sa baƙa wata koriya.

 

47. Daga nai kiran baiti guda sai ga ɗari,

Suka ce da ni don Allah kar kayi turjiya.

 

48. Kafin na ankara sai dubu suka hallara,

Suka ce da ni "mu ma muna daɗa godiya" .

 

49. Yaro ka bini a hankali don na wuce-

Shata wurin waƙar da ba ɗirkaniya.

 

50. Na zarce ‘yan koren mawaƙan zamani,

Na san Mu'azu, Aƙilu kaji mazan jiya.

 

51. Na san Sa'adu gwani wurin zuba baituka,

Ballantana Ala da ke mini rakkiya.

 

 

 

52. Ni sunka bauta ko ga waƙar in sukai,

Balle su Hauwa gwaram ɗiya jaririya.

 

53. To dukkaninsu kana aje su wuri guda,

Dolen su ne da muƙarrabansu su sunkuya.

 

54. Su fake da baiti na guda da na ƙirƙira,

Su tsaya su karɓi tabarraki suyi kwaikwaya.

 

55. Kalle ni nan a cikin ido na mai ka ga,

Na kwan dubu ba gyangyaɗi ga idaniya.

 

56. Zo kalli takalman da ke bin ramuka,

Ko su sukanyi dubu haɗewar ƙafiya.

 

57. Ni ɗai ka cinna wuta a kundin baituka,

Kafin subahi na zubo wa zai iya?.

 

58. Damar ka yanzu ka bini sannu a hankali,

    Da na saka ka cikin mawaƙa ka iya.

 

59. Shin za ka tashi ka tattare ne ko ko dai?

Sai na saka yaran ga sun maka dariya.

 

60. Waƙa gida na ne a barni na fantama,

Ni ne kaɗai sarkin da babu sarauniya.

 

Aminu(Abu Isah Asshankidy)

61. Shin wanga waƙe ne ko ko hakan?

Maganarka ce don duk ciki kwakyariya.

 

62. Wake batun wani sha'iri in dai dani,

Ni ne nake watse shirusu gaba daya.

 

63. Domin idan har nayyi baiti na guda,

A cikin dare tuni ya bazu kan safiya.

 

 

64. Lambar yabo aka ban nace ni bani so,

Domin kwa ni wahayi ake min kun jiya.

 

65. Ya zakayo waƙe ka zan dai dai dani?

Kai haƙƙuri ya ɗan uwa don na iya.

 

66. Ni ne nake waƙar siyasa don kuji,

Wasu ma suyo koyi waɗansu su rairaya.

 

67. Dukkan fagen waƙe fa ni duk na iya,

Jigonta duk na yo fice ban zamiya.

 

68. A fage na so ni ne ka waƙe sai ka ce,

Majnunu laila shugaba tun can jiya.

 

69. A fagen Habaici ko ko zambo Kar ka yo,

Wasa dani domin kwa zanma kwaf ɗaya.

 

70. Waƙe wuri na ni fa koda shan ruwa-

Ya fi shi domin shan ruwa da akwai wuya.

 

71. Ita ko da zar na buɗe baki zaku ji,

Baiti guda,baiti dubu ba Turjiya.

 

72. Ga tambaya amsarta ban domin nasan,

Kai sha'iri kake wanda yassan ƙafiya.

 

73. Shin sha'irai nawa ne a can suka san da kai?

Suka ce “da kyau waƙarka tai” ba Tankiya.

 

74. Ko da kwa mun duba Bama same su ba,

Baka cikin Duk sha'irai fa gaba ɗaya.

 

75. Kai haƙƙuri ya ɗan uwa kai laddabi,

Don in kayo wasa dani ka malgaya.

 

 

 

76. Don sha'irai basa barin mai ja dani,

Wane mutum ya wuce yaje ga samaniya.

 

77. Karma ka fara batun ka zam dai dai da ni,

Domin kwa kuka zakayo da idaniya.

 

78. Duk sha'irai sunzo garen sun miƙa kai,

Suka ce gwani kayyo tayi dan ka iya.

 

79. Domin haka ya ɗan uwa ga shawara,

Kai haƙƙuri kai ma ka miƙo min wuya.

 

80. In kaƙi bi to Sha'irai sun bi maka,

Ni ne ka mulkin duniyar yin ƙafiya.



Daga Alƙalamin
Muhammad Muktar (Maisugar)
Da
Aminu Sani Uba (Abu Isah Asshankidy)
aminusaniuba229@gmail.com
08162293321, 09123098967, 07034370481

Post a Comment

0 Comments