Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙe mai taken “IN AN BUGI JAKI A BUGI TAIKI ” Daga alƙalamin ABU ISAH AMINU SANI UBA ASSHANKIDY

1. Ni da sunan kaliƙinmu,

Ga ya nan saƙo garemu.

 

2. Yau da mi'iyya nazo ni,

Zan batu ne kan ƙasarmu.

 

3. Ɗan uwa zo nan kaji ni,

Dan mu zamto kare kanmu.

 

4. Mun shiga uku nan ƙasarmu,

Munyi  kuka  ba a jinmu.

 

5. Munyi wayyo munyi wayyo,

Babu mai kula duk kiranmu.

 

6. Kar mu zargi shuwagabanni,

Mu mukai cuta wa kanmu.

 

7. Dan kwa munce bamu zaɓar,

Wanda zai gyaran ƙasarmu.

 

8. Mu nufin a bamu Naira,

Sai mu bayar ƙurri'unmu.

 

9. Ba tsayawa mui tunanin-

Yin hakan mai zaya bamu.

 

10. Sai ilahu ya zare hannu,

Sai ya barmu mu ƙwaci kanmu.

 

11. Ga shi ko duk munyi laushi,

Har  fita  na  gagararmu.

 

12. Gashi koda munyi noma,

          Bamu noman yaiishe mu.

 

13. Kasuwanci babu riba,

Don kwa cuta ce a ranmu.

 

14. Gashi bamu ruƙon amana,

Kunga mu muka cuci kanmu.

 

15. Shugabanni na gwaramu,

Basu ko tuna ƙauyukanmu.

 

16. Ko garin ma ba ruwansu,

Babu tsarin taimakonmu.

 

17. Ga shi koda munyi boko,

Mun gama ba mai kula mu.

 

18. Ku ku ce kuma muyyi bokon,

Dan muyo gyaran Ƙarsarmu.

 

19. Gashi munyo babu aiki,

 Ba sana'ar kare kanmu.

 

20. Daga nan wasu sai fasadi,

  Sai su dawo sukkashemu.

 

21. Koda yaushe sui fakonmu,

Dan su samu kuɗi wurinmu.

 

22. Ko a kawo ko su yanka,

Ko su barmu da rayuwarmu.

 

23. Amma kuwa shi mutunci,

Sun zubarwa ‘yan uwanmu.

 

24. Sunyi fyade aggaresu,

Sun buge su cikin gidanmu.

 

25. Wani ma a gaban ɗiya tai,

Ko  iyali  za  su  karmu.

 

26. Wani sa'in subbugemu,

Ga   iyali  na  ganinmu.

 

27. Ba su ikon yin kataɓus,

Babu komai ‘yan uwanmu.

 

28. Don kwa mune ja wa kanmu

           Don fa nan a cikin ƙasarmu-

 

29. Shugabanni ba ruwansu,

Basu tausan rayukanmu.

 

30. Ba ruwansu mu kwan da yunwa,

Ko  da   jinya  ajjikin mu.

 

31. Ko karatu nan ƙasarmu,

Dakkuɗinmu muke abinmu.

 

32. To idan mun gane wannan,

Ba batun wai za'a bamu-

 

33. Ayyuka a cikin Ƙasarmu,

Sai mu dawo taitayinmu.

 

34. Duk muzo mu riƙe sana'a

Don mu tsira da rayuwarmu.

 

35. Kunga kenan koda aiki,

Ko rashi nai ba ruwanmu.

 

36. Zamu rayu cikin salama,

Babu mai cin zarrafinmu.

 

37. Babu me cewa muzomu,

Don mu sheƙe ‘yan uwanmu.

 

38. Don muna da kuɗin abinci,

Babu yunwa ajjikinmu.

 

39. Daga nan kuma babu ɓarna,

Ba kisan kai accikinmu.

 

40. Ba batun (kidnaf) cikinmu,

Mun riga mun kare kanmu.

 

41. Shugabanni ga ya saƙo,

Kar ku manta kaliƙinmu.

 

42. Shi ya baku riƙon ƙarsarmu,

Don ku kare rayukanmu.

 

43. Kunyi kamfen dan mu baku-

Dangwalenmu ku hau samanmu.

 

44. Kunyi Alƙawari na ƙarya,

Zaku kare yan Ƙasarmu.

 

45. Zaku kauda dukkan talauci,

Zaku yaye fargabarmu.

 

46. Kana aiki zaku bamu,

Ba zaman banza cikinmu.

 

47. Haka nan zamui karatu,

Babu ko sisi kuɗinmu.

 

48. Gashi yau a cikin ƙasa ta,.

Da kuɗin ya gagaremu.

 

49. Don karatun yayi tsada,

Shin ina wai zaku kaimu?

 

50. Ga shi kunce lafiyarmu,

Babu mai kuka cikinmu.

 

51. Ko kwa dama kun faɗa ne,

Don kuyo cuta garemu.

 

52. Haka nan kuka ce ruwa ma,

Zai wadata cikin garinmu.

 

53. Dukka kauye dukka saƙo,

Zamu warwasa rayuwarmu.

 

54. Ba wutar (NEPA) ƙasarmu,

Gashi kunce zamu Samu.

 

55. Ba wutar kuma ba ruwan duk,

Munyi Two Zero ku ji mu.

 

56. Ga ƙasarmu da arziƙinta,

Kun riƙe sam baku bamu.

 

57. Tituna sam babu kyawu,

Can ga hanya attaremu.

 

58. Ko kuɗi ko mui ta ranmu,

Ba ruwanku da rayukanmu.

 

59. Ga shi harkar nan ta noma,

Tallafin mu ba a bamu.

 

60. Shugabanni karku manta,

Ranstuwa kunyo gabanmu.

 

61. Zaku taimaki al'umarmu,

Aiyyuka kuma zaku bamu.

 

62. Ga shi dai Allahu yaso,

Kar kuyo nisa ku barmu.

 

63. Kar ku tare can Abuja,

Mu kwa nan ƙauye ku barmu.

 

64. Mui ta holoko abinmu,

Babu mai sisi cikinmu.

 

65. Ga matasa nata yawo,

Sun zamo matsala garemu.

 

66. Su suke dukkan fasadi,

Su suke sata garinmu.

 

67. Ba sana'a babu aiki,

Kaga kwai matsala ƙasarmu.

 

 

68. Yan siyasa kuiwa Allah,

Kar kuyo nisa ku barmu.

 

69. Kun riga kun ɗau Amana,

Kar ku bar kishin Ƙasarmu.

 

70. Kui ta aiki kui ta aiki,

Yin hakan ne taimakonmu.

 

71. Daga nan kuma zamu gane

Ɗan halak waye cikinmu.

 

72. Zamu gane mai Butulci,

Mai shirin cuta garemu.

 

73. Wanda sam sam baida kunya,

Za ya dawo nan wurinmu.

 

74. Za ya zo nema wajenmu,

Maga Mai bi nai cikinmu.

 

75. Za ya gane yan halak ne-

Mu ga duk mai taimakonmu.

 

76. Ga mu dai wai mu da yanci,

Ga ƙasashe sun wuce mu.

 

77. Sunyi nisa gamu baya,

Baku sam kishin ƙasarmu.

 

78. Ga shi tare anka bamu,

Dukka ‘yanci mun zamo mu-

 

79. Ga mu can mu ne a baya,

ba shirin gyara ƙasarmu.

 

80. Can a farko shugabanni,

Yan mazan jiya masu sonmu.

 

81. Sunyi aiki babu wasa,

Duk shirinsu ginin ƙasarmu.

 

82. Jami'o'i sun ginawa

Dan ginin goben ƙasarmu.

 

83. Asbitoci gasu nan duk,

Dan kulawar lafiyarmu.

 

84. Kamfanoni ko ina duk,

Ba zaman banza cikinmu.

 

85. Babu sata babu cuta,

Sunyi aiki aggaremu.

 

86. Ga wasunsu na ambace su,

Ɗan tafawa uba wurinmu.

 

87. Shi ya sa ɗanba ta gyara,

Gashi yau mun samu kanmu.

 

88. Babu shi wasu sun kashe shi,

Sunyi  cutarwa   garemu.

 

89. Amadi Sardauna zaki,

Can yana nan zuciyarmu.

 

90. Adu'ar kairi muke mar,

Ya yi aiki nan ƙasarmu.

 

91. Ya ilahu abun nufi na,

Gamu nan duk ‘yan Ƙasarmu.

 

92. Munyi roƙo duk gareka,

Dan kwa kasan duk halinmu.

 

93. Kar ka barmu da namu wayo,

 Ya gwaninmu ka taimakemu.

 

94. Daga ƙarshe nai salati,

Gun Muhammadu shugabanmu.

 

95. Har da Ali dama sahabu,

Wanda su ne fittilunmu.

 

96. Zana sa aya na nisa,

Can fa Ringim ne garinmu.

 

97. Nassarawa unguwarmu,

Nan da kaje ga gidanmu.

 

98. Gata nan baiti Ɗari cif,

Nayi bulala garemu.

 

99.  Ni Aminu ake kirana,

Mai burodi uba garemu.

 

100. Hamdala nai wa ilahi,

Kaliƙi sarki gwaninmu.

 


ABU ISA ASSHANKIDY
Aminu Sani Uba Ringim
08162293321
Aminusaniuba229@gmail.com

Post a Comment

0 Comments