Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwankwalati

5.20 Ƙwanƙwalati

Wannan wasa ne da ya zo ƙasar Hausa bayan cuɗanyar Bahaushe da baƙin al’ummu, musamman Turawa. Domin kuwa, yara na kwaikwayon yadda ake ƙwallon ƙafa ne (tambola) a cikin wannan wasa. Wato akan bi dokoki irin na ƙwallon ƙafa yayin gudanar da wasan. Akwai kayan aiki da ake buƙata kafin gudanar da shi. Sannan ba ya tafiya da waƙa. Ana gudanar da wannan wasa ne tsakanin yara biyu. Idan suka wuce haka, saura za su jira ne. Duk wanda aka cire, sai wani daban ya shiga gurbinsa.

5.20.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Ba a keɓe wani wuri na musamman ba da ake gudanar da wannan wasa. Sai dai ana buƙatar wuri mai siminti kafin a iya gudanar da shi.

ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma ko da dare. Abin da ake buƙata kawai shi ne a samu wadataccen hasken da za a iya kallon ‘ya’yan wasa da kuma ƙwalluwa.

5.20.2 Kayan Aiki

i. Ƙwanƙwalati

ii. Takarda ko cingam

iii. Faleti

iv. Ƙwalluwa

v. Gola

vi. Manyan batira narediyo domin haɗa fos

vii. Leda fara ko wani abu mai kama da wannan a matsayin raga

viii. Ƙananan duwatsu domin danne raga

ix. Gawayi ko alli domin zana fili

5.20.3 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tanadi kayan aiki da aka bayyana a sama ƙarƙashin 5.65.2. Za su tsara filin tsaf, tamkar filin wasan ƙwallo na sali. Kamar yadda aka bayyana a sama, dokokin wannan wasa daidai suke da dokokin wasan ƙwallon ƙafa. Saboda haka ana gudanar da wasan ne tsakanin garuruwa biyu.

Akan sanya ‘yayan wasa guda goma sha ɗaya a kowane gida. Guda goma suna ciki, ɗaya kuma shi ne gola. Za a riƙa yin amfani da faleti wurin buga ‘yan wasa. Wato mai wasa zai ɗora faletinsa a gefen ɗan wasa ta sama, sannan ya ɗan danna da ƙarfi. Ƙarfin dannanawar ya danganta da iya gudu da kuma ƙarfin tafiyar da yake so ɗan wasan da zai buga ya samu. Idan yana so ɗan wasan ya je wuri mai nisa ne, to da ƙarfi zai danna. Idan kuma ɗan gusar da shi kawai yake son yi, to zai danna kaɗan. Wannan ƙwanƙwalati da ake bugawa shi zai je ya bugi ƙwalluwa. Saboda haka, akan yi amfani da ɗa da ya fi kusa da ƙwallowa ne yayin da za a buga.

A cikin wasan ƙwanƙwalati akan yi fasin da hedin da fenalti da firi-kik da kwana da turowin da ma sauran abubuwan da ake yi a cikin wasan ƙwallon ƙafa. An yi bayanin irin waɗannan kalmomi cikin jerin kalmomin da aka yi bayaninsu a farkon littafin.

Wani abu da ake yi yayin wasan ƙwanƙwalati wanda ba a san da shi a ƙwallon ƙafa ba shi ne konsef. Wannan dai yanayi ne wanda mai wasa ya buga ƙwalluwa, ƙwalluwar kuwa ta bugi wani ɗan wasa daban, wanda hakan ya canza mata wurin da ta nufa da. Dukan wani ɗan wasa daban da ta yi shi ake kira koncef. Idan filin wasa ya mannu da gini ta gefe guda, akan yi konsef da ginin.

Yayin da aka zura ƙwalluwa cikin raga, to an sha ke nan. Mai wasa kuma zai iya yin ƙeta. An fi yin ƙeta a yayin da mai wasa ya ga abokin wasansa zai sha shi, sannan ba zai iya buge ƙwalluwar ya hana shi sha ba. A irin wannan yanayi, zai seta ɗan wasan da abokin wasarsa zai yi amfani da shi wurin sha, ya jambaɗe shi a maimakon bugun ƙwalluwa. Hakan zai sa wannan ɗan wasa ya turu gefe guda, musamman idan cikon da aka masa ba mai nauyi sosai ba ne.

Yayin da aka yi ƙeta cikin wasa, to akan buga ƙeta. Idan a cikin etin ne, to fenalti za a yi, wato bugun daga kai sai gola. Idan kuwa wajen etin ne, to za a yi firi-kik. Yayin da za a buga firi-kik wanda zai buga zai jira abokin wasansa ya jera ‘ya’yan wasa a gaban ƙwalluwar da za a buga, bayan an ba da tazarar taku guda nahannu. Wani lokaci har zai ɗora wasu ‘yan wasan a kan wasu, gudun kada ƙwalluwar ta wuce ta saman ‘yan wasan.

Akan yi turowin yayin da kwalluwa ta fita. Takan fita ko dai bisa kuskure ko yayin da mai wasa ya tura ta gudun kada a sha shi. Lokacin da za a yi turowin, kowa zai gyara ‘ya’yan wasansa. Wato ya canza musu wuri ya aje kowanne a wurin da yake so. Mai wurga turowin kuwa, zai ajiye ‘yar wasar da zai wurga turowin da ita bisa layi ta daidai wurin da aka fitar da turowin ɗin. Zai kuma ɗora ƙwalluwa bisa wannan ‘ya. Sai kuma ya buga ‘yar yayin da ƙwalluwar ke samanta. Saboda haka, ƙwalluwar da kuma ‘yar za su tafi a tare.

Yayin da mai wasa ya fitar da ƙwalluwa ta ɓangaren gidansa kuwa, ko kuma ƙwalluwa ta taɓa ‘yarsa kafin ta fita lokacin da abokin karawarsa ya bugo ta, to za a ɗago masa kwana. Yayin ɗaga kwana, masu wasa suna da dammar ajiye ‘ya’yan wasa a wurin da suke so. Mai ɗago kwana kuwa zai je dungu ya ɗago, tamkar yadda ake yi a wasan ƙwallon ƙafa.

5.20.4 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta bunƙasa tunani da dabara gare su. Za a tabbatar da hakan lokacin da aka ga yadda masu wasan ke nazarin hanyoyin da za su bi domin cin nasara a wasan. Sai dai kwaikwayo ne kai-tsaye aka yi na wasan ƙwallon ƙafa da ta zo wa Bahaushe bayan cuɗanyarsa da Turawa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA 

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments