Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Tatsuniyar Hausa
Wannan littafi mai suna “Tatsuniyar Hausa” an rubuta shi ne don a yi waiwaye adon tafiya a kan abin da ya shafi tarbiyyar ‘ya’yan Hausawa. Tun lokacin da Hausawa suke cikin Maguzanci har farkon shigowar addinin Musulunci a ƙasar Hausa, tatsuniya tana cikin makarantun farko, da ‘ya’yan Hausawa ke koyon dangogin tarbiyya, kamar ladabi da biyayya, tsare gaskiya, barin yin ƙarya a cikin zance, taimakon juna, rashin haɗama da sauransu.
Haka
kuma tatsuniyoyi a wancan lokacin suna samar da nishaɗi na musamman ga
Hausawa, ta hanyar ban dariya da waɗansu al’adun da suke tare da su,
kamar na ɗaure gizo don gudun
mutum ya yi ɗemuwa (makuwa) da
koyar da tsafta da sauran muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarmu ta yau da
kullum.
0 Comments
Post your comment or ask a question.