Ticker

6/recent/ticker-posts

Tatsuniyar Dan Ba-Ka-Jin-Bari

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

Tatsuniyar Ɗan Ba-Ka-Jin-Bari 

Gatanan – Gatananku

Wata tsohuwa ce ta ga ƙurji ga yatsanta, sai ta ce “bari in fashe shi”. Tana fashewa, sai ta ga wani yaro ya fito! Wannan yaro ya tashi wani irin ƙiriritacce marar jin magana, duk abin da yake so shi yake yi, ba a iya hana shi, wannan ne ya sa ta sa masa suna “Ɗan-ba-ka-jin-bari” Daga baya, sai ta sake samun ciki ta haifa masa ɗan ƙane. Wata rana da suka kwanta kwana, sai ɗan ƙanen yana mai nishi daidai kunnensa.

Tatsuniyar Ɗan Ba-Ka-Jin-Bari

Sai ya ce, “mama kin ga ɗanki yana man nishi ga kunne” Sai mamar ta ce, “ƙyale shi”, sai ya ce “mama wallahi bai bari ba”. Sai ta ce, “kai ka kashe shi to” Tana masa gatse, shi kuma da yake bai jin gatse, sai ya ɗauke shi ya tafi da shi bayan ɗaki ya kashe shi.

Ko da ya dawo, sai ya ce “Mama na kashe shi”, sai ta ce “ka yi me?” Sai ya ce “na kashe shi” Sai ta kama shi ta zane shi da bulala.

Tatsuniyar Ɗan Ba-Ka-Jin-Bari

Sai ya fita waje yana kuka! Yana nan sai ga wani mutum ya zo zai wuce ya tarar da shi yana kuka, sai ya ce, “kai, Ɗan-ba-ka-jin-bari, me ya sa kake kuka?” Sai ya ce “wai mama ce don na taɓa mata ɗanɗa shi ne ta buge ni”. sai mutumen ya ce, “to zo ka yi mini tsaron gangunana”. Yana cikin tsaron gangunan, sai ya ɗauki ƙatuwar gangar ya sayar da ita, ya sawo nama da kuɗin, suka ci, har tare da shi mai gangar. Bayan wani lokaci da wannan mutumin ya duba bai ga gangarsa ba, sai ya ce “kai Ɗan-ba-ka-jin-bari ina gangata?” Sai ya ce “naman da ka ci jiya ubanka ya baka shi?” ko uwarka ta ba ka shi?” Da ya fahimta cewa gangarsa ya sayar ransa ya ɓaci sosai, don wannan gangar ita ya fi so da kowace ganga daga cikin gangunansa. Ya sami bulala ya ba shi kashi, kuma ya kore shi.

Tatsuniyar Ɗan Ba-Ka-Jin-Bari

Daga nan sai wani mutum ya zo wucewa ya tarar da shi yana kuka, ya tsaya, ya tambaye shi, ya ce kai “kai Ɗan-ba-ka-jin-bari ko kana yi man gadi?” Ya ce “eh”, sai suka tafi gidansa, ya sa shi ya tsare mai kofar gidansa, kamar dai yadda masu gadi suke yi. Bai daɗe yana yi ba sai ya ɓanɓare kofar gidan ya sayar, ya sawo nama da kuɗin, har suka ci tare da maigidansa, ba tare da ya sani ba! Lokacin da ya gane sai ya tambaye shi ya ce “Ɗan-ba-ka-jin-bari ina kofata?” sai ya ce “naman da ka ci jiya ubanka ya baka shi?” ko ko “uwakka ta ba ka shi?” Nan take sai shi ma ya ba shi kashi kuma ya kore shi!

Tatsuniyar Ɗan Ba-Ka-Jin-Bari

Sai ya fita waje yana kuka! Yana nan sai wani malami ya zo ya ce “kai Ɗan-ba-ka-jin-bari mi aka yi maka?” sai ya ce “wai daga na taɓi kofarsa shi ne ya koreni”, wannan malamin ya tausaya masa har ya ce “zo in baka tsaron fadar sarki” sai suka tafi suka haye saman icce don ya nuna masa yadda aikin yake. Suna saman sai suka ga sarki ya yo aski wanda ake ce ma ƙwal kwabo[1], sai Ɗan-ba-ka-jin-bari ya ce “ka ga bolar shege?” “koh in mata kashi?” Malamin yana hana shi, amma ya ƙi ji, Sai ya yi mata kashi! yana saman icce! har sarki ya lakato shi ga fuskarsa, sarki fa ya harzuƙa ya ce sai an kamo su! Wannan ya sa sun shiga cikin wani mawuyacin hali na firgita da tsoro da tashin hankali. Suna cikin haka sai wata tsunsuwa ta zo wajen su ta ce “in taimake ku?” Sai suka ce “eh” sai ta ce “ku zo ku hau bayana in tashi da ku don kar sarki ya sa a kama ku a kashe ku”, ta ce “amma kar a soke ni saboda duk aka soke ni ruwa zamu faɗawa!” Suka amince suka hau bayan tsuntsuwa, Bayan tsuntsuwa ta tashi da su Ɗan-ba-ka-jin-bari ya ce ma malam “wallahi soke ta zan yi”, malam ya ce “don Allah kar ka soke ta”, amma ya ƙi ji, sai ya sa sanda ya soke ta,  ai kuwa sai Ɗan-ba-ka-jin-bari ya faɗa ruwa!

         

Tatsuniyar Ɗan Ba-Ka-Jin-Bari

Da shigarsa cikin ruwa sai ya iske ‘yan ruwa, da ma suna neman wanda zai riƙa tsare masu ɗiyansu don su tafi wurin kiyo, su ma sai suka neme shi da ya zo ya tsare masu ‘ya’yansu, nan take ya amince zai tsare masu har su tafi wurin kiyo su dawo, su kuma suka bar shi da su suka tafi. Ana nan sai Ɗan-ba-ka-jin-bari ya ce wa ‘ya’yan “ku zo mu yi wasan daka”, sai suka zo, ya ce “bari in fara shiga ku daka ni kaɗan-kaɗan”, ya shiga suka daka shi kaɗan-kaɗan, sai ya fito suka shiga, da farko guda bai shiga ba sai ya ce masa “kai baka shiga?” yana shiga sai ya fara daka su kaɗan-kaɗan, daga baya sai ya rafke su ƙwarai, ya dake su ya soye su! Ko da uwayensu suka dawo suka iske ya soye nama ya ce “ku taho mu ci tare” sai suka fara ci, sai can suka ce “bari mu rage ma ɗiyanmu,” sai Ɗan-ba-ka-jin-bari ya ce “ku dai ku cinye tunda dai ba su gani ba”, sai suka ce “kai Ɗan-ba-ka-jin-bari ina ɗiyanmu?” sai ya ce “naman da kuka ci uban ku ya baku shi?” “ko uwarku ta baku shi?” Da suka fahimci abin day a yi sai suka ɗaure shi, suka je su samo buloli don su ba shi kashi, yana nan ɗaure sai ga kurar ruwa ta zo wucewa, da ta gane shi sai ta ce “kai Ɗan-ba-ka-jin-bari mi ka yi aka ɗaure ka?” shi kuma sai ya ce “wai don dai na ce ban cin nama shi ne suka ɗaureni”, sai kura ta ce “bari in kwance ka ni ina cin naman”, sai ta kwance shi, ta ce kai ka ɗaure ni, ka je ka ɗauko naman da baka ci, sai ya ɗaure ta, idan ta ji inda bai ɗauru ba sai ta ce “nan bai tsuku ba”, sai ya ƙara ɗaure ta. Sai da ya ɗaure ta tsaf, ya tsere bai ko waiwayo ba.

Tatsuniyar Ɗan Ba-Ka-Jin-Bari

Ana nan sai ta fara ganin inuwar bulala, sai ta ce “Ɗan-ba-ka-jin-bari ban iyawa kwance ni”, ina! Ai Ɗan-ba-ka-jin-bari ya gudu ya bar kura a ɗaure! Ko da suka zo suka iske kura a ɗaure, sai suka bata kashi tana ta zawo, tana ƙugi har suka kashe ta. Shi kuma Ɗan-ba-ka-jin-bari ya tafiyarsa ya koma gida ya tuba ga mamarsa har ta yafe masa, ya cigaba da zamansa lafiya, ya daina yin duk wani abin da bata sa shi ba.

Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

Tambayoyi

1. Mene ne dalilin da ya sa aka sa wa tauraron wannan tatsuniyar suna Ɗan-ba-ka-jin-bari?

2. Ko wannan sunan na Ɗan-ba-ka-jin-bari ya dace da shi? Kawo dalilai

3. Waɗanne darusa aka koya daga wannan tatsuniya?[1]  A aske dukan gashi, kan mutun ya yi kwal. 

Post a Comment

0 Comments