Ticker

6/recent/ticker-posts

Gabatarwa - Data Littafin Tatsuniyar Hausa

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

Gabatarwa

An yi tunanin rubuta wannan littafi ne saboda a taskace tatsuniyoyinmu na Hausa daga barazanar da suke samu ta zamananci, na ɓacewarsu daga rumbun tunanin mutane, har su manta da su da muhimman abubuwan da suke a ƙunshe a cikinsu. Haka kuma an rubuta shi ne domin a samar da wani abin amfani wajen koyo da koyar da Hausa a makarantun furamare da na gaba da su a wannan yanki na ƙasar Hausa. 

An yi ƙoƙarin kawo wasu hotuna a kan abubuwan da ke faruwa a cikin tatsuniyoyin a wasu wurare domin jawo hankalin yara su himmatu,  kuma su yi sha’awar tatsuniyoyin, su riƙa ganin abin kamar ana aiwatar da shi ne a fili.

A ƙarshen kowace tatsuniya da aka kawo an samar da wasu tambayoyi domin auna fahimtar ɗalibai a kan darussan tatsuniyar da aka kawo. Saboda haka, idan malami zai koyar da tatsuniya, sai ya gaya wa ɗalibansa cewa akwai wasu tambayoyin da zai tambaye su a ƙarshen tatsuniyar don kar su karkatar da tunaninsu.

Post a Comment

0 Comments