Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University
Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna
Umar Bunguɗu
(Sarkin
Gobir Na Bunguɗu)
Email:
harunaumarbungudu@gmail.com
Phone:
08065429369
Muƙaddima
Wannan littafi mai suna “Tatsuniyar Hausa”, daga sunansa ya fitar da maƙunsarsa. Littafi ne da ya ƙoƙarta wajen adana da kuma tunatar da mu wani ɓangare na tatsuniyoyin da suke tare da mu a tsawon shekaru, amma saboda canzawar zamani suke neman su ɓace ɗungum.
Saboda haka, ba tare da na yi wani dogon surutu ba, zan iya cewa, wannan ɗan littafi wata taska ce mai muhimmanci ga yara, da ma duk wani wanda bai yi tu’ammali da rayuwar zama da kakanni ko amare ba. Littafi ne da ya bayyana muna yadda jiya take, domin amfanin yau da kuma gyara gobe.
Ba ko tantama, wannan littafi zai zama wata sabuwar makaranta ce ga yaran yanzu, zai kasance abin saka nishaɗi da walwala ga waɗanda suka sadu da shi. Da fatar niyyar da marubucin ke da ita game da assasa wannan aiki ta cika, buƙatarsa ta biya, ba a nan doron duniya ba, har gobe ƙiyama.
Daga ƙarshe, ina kira ga duk waɗanda Allah ya ba dama da su sayi wannan littafi ko don su karanta ko su ba wani ya karanta a gida ko a makarantunmu, ko kuma domin su taimaka wa wannan ƙoƙari na Dokta Haruna Umar Bunguɗu ya ɗore. Allah ya ƙara taimakawa. Amin.
Dokta Yakubu Aliyu Gobir
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.