Ticker

6/recent/ticker-posts

Gamda'are

Zumu /Ɗan Uwa na ji ni. Ko a wannan Waƙar wanda aka ce ma Sarkin Ƙaya Tambari Gamda'aren shi watau Sarkin Rafin Dosara (Gamda'aren Sarkin Rwahi) ɗan uwan shi ne na jini domin duk wanda ke Sarautar Dosara ya na iya zamowa Sarkin Ƙayan Maradun. Bayan rasuwar Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi, Sarkin Ƙayan Maradun na biyu da ya biyo bayan shi ɗan shi ne, Alhaji dake sarauta a Dosara da laƙabin Sarkin Rafi.

Idan ka saurari Waƙar Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ta Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello GCON KBE mai amshi 'Kada Marake Giwa.. Ya na cewa "Gamda'aren Sarkin Musulmi, na Alƙalin Alƙalai manyan Hausa Uban Janjuna.. /Kaga Sarkin Musulmi Abubakar III ɗan Uwan Sardaunan Sakkwato ne jini domin dukan su daga Zauren Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio suka fito. Sarkin Musulmi Abubakar III ɗan Modibbo Usman ne, Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ne, Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne. Sardauna Ahmadu Bello ɗan Sarkin Raɓah Ibrahimu ne, Sarkin Raɓah Ibrahimu ɗan Sarkin Yan Shawara(Zartu Yan Shawara) /Sarkin Raɓah /Sarkin Musulmi Abubakar II (Mai Raɓah) ne, Sarkin Musulmi Abubakar Mai Raɓah ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne.

Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya na cewa "Mai Gusau raba kaya, ba a kaima ka wargi, Mai rabo da yawa gamda'aren Sarkin Gobir" a cikin Waƙar shi ta Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar / Hakimin Gundumar Gusau, Marigayi Sarkin Kudun Gusau, Alhaji Sulaiman Ibrahim Isa. Gamda'aren Sarkin Gobir na Isa Amadu I ya ke nufi. Da Sarkin Gobir na Isa Amadu I da Sarkin Kudun Gusau, Alhaji Sulaiman Ibrahim Isa daga gida suka fito Zuriyar Sarkin Musulmi Aliyu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments