Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Karkata Kan Amarysa, Ina Neman Shawara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm mln Allah yasaka maka da mifificin alkhairi. Dan Allah mln inada tambaya mijina ne yayo aure to daman tun kafin yayi auren banajin daɗin shi to shi ne yanzu kuma yayi to Amman ya karkata kan amaryar shi ne ake ta ce man in je in nemi taimako ba haramun ba ne har ma danginshi haka suke cewa to mln mene ne shawararka a gare ni nagode ƙwarai.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Masu Cewa ki je wurin Malami Sune Shaiɗanun Mutane da Allah Yake Faɗi. Masu ingiza mace ta kaucewa hanyar Allah da ManzonSa Sabida haka Kar ki je Wurin Wani Malami. Idan kin je ma ko kinyi tsafi da Sihiri ba Abin da zaiyi. Ko yayi ma akwai lokacin da zai warware. Sai a Koma Gidan Jiya. Idan kuma kina sabuntawa. To fa a haka za ki Mutu kina cikin yiwa Allah shirka. Kinga sai ki je chan ki same shi ya Jefa ki a Wuta.

Haka zalika Ba za ki Taɓa Amfanawa Kanki komi ba. Domin duk kuɗinki a wajen Waɗannan Malaman zai ke tafiya.

Shawara A nan Shi ne kiyi masa biyayya. In shã Allahu Zai so ki, So Na Hakika, zai fifitaki fiye da kishiyarki. Kuma na tabbatar Miki indai akwai Biyayya Allah zai ganar da shi ya gane cewar kina yimasa biyayya.

Babu wata hanya mallake miji kamar kyawawan halaye da kyawawan ďabi'u shi miji ana mallakarsa ne ta hanyar ganin girmansa, kyautata masa da yi masa biyayya dasauransu.

Babu yadda za ayi ki samu karbuwa da samun farin ciki a gidan aurenki sai ki tsarkake niyyarki kuma kin yarda cewa shi zaman aure ibadane, matukar kin nemi taimakon Allah za ki samu farin ciki a cikin zamantakewar ki da mijinki.

Akarshe ina shawartar ki lallai ki je ki san hakkokin mijinki da suke kanki sai kiyi ƙoƙarin kiyaye su in sha Allahu za ki mallaki zuciyarsa ba tare da bin waccan hanyar bokayen ba.

Allah shi ne Masani.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments