𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam mallam barka da warhaka Allah ya karawa mallam lafiya da ilimi Mai amfani. Dan Allah Ina da budurwa ba'a sati sai mun samu matsalar a kan wasu halayin ta idan Ina Mata gyara ko nayi Mata wa'azi a kan abin da take sai tace ba wa'azi Zan Mata ba. To yanzu ma idan har naga farin cikinta to wanne abu take so na bata, jiya take tambaya ta wai yaushi rabon da nayi Mata anko ko na saya Mata kayan kwalliya Dan Allah mallam mene ne shawara a kan maganar Aure da ita?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan na
fahimci wani abu a cikin dabi'un wadda kake son aure, tana da wasu halaye guda
biyu na musamman:
1. farko: Tana
da girman kai; Rashin karɓa
gaskiya a lokacin da mutum yake da tabbacin a kan kuskure yake babbar alamace
ta girman kai.
2. Na biyu:
Tana da kwaďayi: Mace mai kwaďayi ba za ta taɓa
wadatuwa da abin da ta mallaka ba, ba zatayi godiya wa hidimarka gareta ba,
kuma ba zaka ga fara'arta ba sai ka ďauko kābāta.
Lullube da
waďannan abubuwa, akwai 'karancin soyayyarka a zuciyarta. Idan mace ta yi nisa
a son namiji, ta kan ɓoye
bukatunta don ta kasance tare da shi, kuma ba zata yawaita neman abin hannunsa
ba koda tana so kuwa, za a samu tausayi a tsakani.
Sannan idan
mace tana sonka so na hakika, cikin sauki zāka iya sarrafa ta, kuma zaka iya yi
mata umarni ta bi, idan kayi mata hani ta hanu. Domin za ta dinga daraja
umarninka don ganin dorewar soyayyarku, koda kuwa ranta be so ba.
Ɗan'uwa!
Mace mai irin waďannan dabi'u ba ta dace da mutumin kirki ba, domin duk macen
da baza ka ga tana aikata laifi ka hanata ta hanu ba, be dace ta kasance
abokiyar rayuwarka ba, domin wajibi ne miji ya kange iyalinsa daga wuta.
Sannan dole ne
ka duba maslahar yaran da zāku haifa idan ka aure ta, shin za ta iya ginasu a
kan tarbiyyar da ake buƙata? Shin za ta koyar da su yin biyayya wa umarnin mahaifinsu?
Don haka abin
da zan baka shawara da shi shi ne kayi mata nasiha, idan bazata gyara halayenta
ba ka rabu da ita, duniya akwai faďi.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.