Haƙiƙa zikiri ko ambaton Allah yana daga cikin mafiya tsarkakan ayyuka da kyawawansu da girmansu kuma mafiya soyuwa a wurin Allah Azza Wa Jalla. Tirmizi da sauransu sun ruwaito daga Abu Darda’u (RA) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ashe ba zan ba ku labarin mafi alherin ayyukanku kuma mafi tsarkinsu (dadinsu) a wurin Mamallakinku kuma mafi daukakawa ga darajojinku kuma mafi alheri gare ku daga ciyarwarku ga zinari da takardun kudadenku ba, kuma mafi alheri gare ku a ce kun hadu da abokan adawarku su doki wuyayenku ku doki wuyayensu ba?” Sai suka ce: “Hakika muna so ka ba mu (wannan labari) ya Manzon Allah!” Sai ya ce: “Zikirin (ambaton) Allah Madaukaki.”
Masu ambaton
Allah, masu tunawa da Allah su ne a kan gaba wurin tafiya don haduwa da Allah
da kuma Ranar Lahira lami lafiya. An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (ﷺ) ya ce: “Masu kadaitawa
sun wuce gaba. Suka ce su wane ne masu kadaitawa ya Manzon Allah?” Ya ce: “Masu
ambaton Allah da yawa maza da masu ambato (da yawa) mata.” Wadannan su ne
-bayin Allah- waɗanda
Allah Ya yi musu tattalin masauki mai girma da lada mai girma. Allah yana cewa
وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ
كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا
“Masu
zikiri (ambato da tuna) Allah da yawa maza da masu zikiri mata, Allah Ya yi
musu tattalin wata gafara da wani lada mai girma.”
Ina roƙon
Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai
iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji
na Alƙur’ani
ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai
الله تعالى أعلم
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ
ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ
ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
****************************
Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************
Telegram
https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx
WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.