𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne
matsayin magidantan da basa sallah, ko matar ko mijin yaya matsayin aurensu
shin sun kafirta ko kuma suna a musulunci?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله والعاقبة للمتقين
ولا عدوان إلا على الظالمين.
Wajibine a kan
mace tazabi miji nagari wanda tayarda da addininsa da dabi'unsa, haka shima
wajibine yazabi wacce ya aminta da addininta da dabi'unta, sallah tana cikin
mafi girman rukunai na musulunci ita cema rukuni nabiyu acikin rukunan
musulunci, Bai halatta mace ko namiji tayarda da auren wanda baya sallah ba
kuma yake wasa da ginshikin addinininsa ba.
Idan mace ta
auri wanda baya sallah kwata-kwata dangane da ingancin wannan auren akwai saɓanin malamai, jamhurdin
malamai sukace auren ingantaccene domin wanda baya sallah bai kore wajabcinta
ba hukuncinsa shi ne musulmi fasiƙi amma bai kafirta ba.
Wasu malaman
kuma sukace wannan auren lalataccene, Domin duk wanda baya sallah kwata-kwata
kafirine ba musulmine ba.
Saidai
adukkanin halayen wacce ta auri wanda baya sallah amma yaƙudurce
wajabcinta baya kafirta saboda baya sallah, ko kuma ita batasan wannan hukuncin
ba, ko kuma agarinsu ana fatawane dacewa wanda baya sallah ba kafiri ba ne
musulmine mai saɓo,
saitayi biyayya gawanda ya ce mata bai kafirtaba daka cikin malaman garinsu, a
irin wannan hali ba'a yi musu hukunci da lalacewar aurensu.
Amma idan
mijin yanayin sallah wani lokacin jefi-jefi wannan ba'ai masa hukunci daya
kafirta.
Shaikul Islam
ibnu taimiyyah rahimahullah ya ce: Mafi yawa daka cikin mutane, amafiya yawan
garuruwa basa kiyaye salloli guda biyar, kuma basa barin sallah gaba ɗaya, saidai wani lokaci su
yi sallah wani lokaci kuma sudena sallah, waɗannan
sune sukeda Imani da munafunci atare dasu, hukunce hukuncen musulunci nazahiri
zasu gudana akansu, wajan cin gado dasauran hukunce-hukuncen musulunci, majmu'u
fatawa (7/617).
Idan miji
yakasance amafi yawan halayensa baya sallah, abin da yake wajibi ga matarsa shi
ne tayi masa nasiha dayi masa wa'azi da tsoratar dashi Allah, harsai yabar
wannan zunubi maigirma, wanda kafircine awajan malamai masu yawa.
Kuma kada
tadebe tsammani wajan maimaita masa nasiha da wa'azi.
Amma nasiha ga
duk wacce mijinta baya sallah kwata-kwata shi ne idan zata iya hakura dashi
tanemi wani to ta hakura taje ta auri wanda yake sallah, domin duk wanda baya
sallah kwata-kwata kafirine.
Atakaice dai shi
ne ma'auratan dabasa sallah, idan kwata-kwata basa sallar babu shakka
kafiraine, idan kuma sunayinta amma jefi-jefi wasu malaman sukace ba su kafirtaba,
amma idan rashin yin sallar shi ne yafi yawa arayuwarsu nanma sunkafirta.
Sannan
matsayin aurensu yana nan ingantacce 'ya'yansu zasuci gadonsu duk wasu hukunce
hukuncen musulunci zai gudana akansu da auren nasu.
Idan su duka
suka zama basa sallah wajibine ga makusantansu su yi musu nasiha da wa'azi
dansu tuba sudawo suna sallah, idan ɗaya
ya amsa ɗaya yaki
amsawa wajibine araba aurensu, idan kuma mijine baya sallar abin da yafi
gamatarsa taje tanemi wani mijin ta aura.
WALLAHU
A'ALAM.
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.