Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zama Da Mijin Da Bayasan Haihuwa Saboda Dawainiyar 'Ya'ya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne hukuncin namijin da bayasan haihuwa saboda tsoran dawainiyar 'ya'ya, mene ne hukuncin zama dashi, shin matarsa zata iya bijiremar tadau ciki ba tare da yasani ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله الذي أنعمنا بلإسلام .

Shaik Usaimeen Rahimahullah ya ce: Abin da ya kamata ga Musulmi shi ne suyawaita nasabarsu gwar-gwadon yanda suka Samu iko, domin hakan shi ne Umarni da Annabi sallallahu Alaihi Wasallam ya fuskantar dashi zuwa Al'ummarsa cikin fadinsa (Ku Auri mata waɗanda kuke ƙauna masu haihuwa, domin nayi alfahari da yawanku ranar alkiyama, Yawan dangi kuma shi ne yawan Al'ummah, yawan al'umma kuma shi ne izzarta da kwarjininta, kamar yanda Allah madaukakin Sarki ya ce: Yana gorantawa Banu Isra'ila:

وَجَعَلْنَاكُمْ أَكْثَرَ نَفِيرًا... {الإسراء،/ ٦ }

Muka sanyaku Masu yawa cikin mutane.

Annabi Shu'Aibu Alaihissalamu yacewa mutanensa.

وَاذْكُرُوا إِذْ كُنْتُمْ قَلِيلًا فَكَثَّرَكُمْ ۖ ... {الأعراف /٨٦}

Kutuna sanda baku dayawa Allah yayawaitaku

Babu wanda yake inkarin yawan al'umma shi ne sababin izzarta da karfinta mai-makon yanda masu mugun zato suke suranta waɗanda suke ɗaukar cewa yawan al'umma shi ne dalilin dake kawowa Al'umma talauci da yunwa.

Lallai Al'Ummah intayi yawa tadogara ga Allah, tayi Imani da Alkawarinsa zai azurtata komai yawanta kamar yanda yazo cikin fadinsa:

وَمَا مِنْ دَابَّةٍ فِي الْأَرْضِ إِلَّا عَلَى اللَّهِ رِزْقُهَا... {هود /٦}

Babu wata halitta face arzikinta yana wajan Allah

Face Allah ya saukake mata Al'amuranta ya wadatata daka falalarsa.

Dan haka bai kamata mace tayi amfani da kwayoyin hana ɗaukar ciki dasunan tsarin iyali ba saida sharudda guda biyu.

1. Nafarko: Yakasance tana cikin buƙatar hakan dole, kamar ba ta da lafiya bazata iya ɗaukar ciki kowacce shekara ba, ko mai siririn jikice ko kwan-kwaso, ko tana da wasu ababe dazasu hanata ɗaukar ciki kowacce shekara.

2. Na biyu: Mijinta yayi mata izinin tasha, domin miji yanada hakkin a kan 'ya'ya da ɗaukar ciki, sannan dolene sai anshawarci likita a kan waɗannan kwayoyin, shin shansu yana cutarwa kobaya cutarwa.

Idan sharudda biyunnan suka cika, Babu laifi amfani da kwayoyin hana ɗaukar ciki, Saidai hana ɗaukar cikin naɗan wani lokaci, bawai na din-din har abada ba, domin wannan akwai yanke yaduwar al'umma acikinsa.

fatawa Mar'atul musulimah (2/ 657-658).

 Illah da cutar dashan wadannan kwayoyin suke haifarwa Shaik Usaimeen ya ce: Labari ya iskeni daka bangarori dayawa daka likitoci damasu bada magani cewa kwayoyin hana ɗaukar ciki suna cutarwa, tabangarenmu munsan illarsa, domin hana wani abu na dabi'ah da Allah yahalicci mutum akansa yakuma rubutawa matan 'yan adam babu kokwanto wannan cutarwane, Allah maɗaukakin sarki mai hikimane, bahaka kawai yasa jini ke fita daka jijiyoyiba awani lokaci sananne saida hikima, kasancewar Mukuma muna hana haka da wannan magun-guna cutane babu shakka.

Labari yariskeni abun yawuce yanda ake siffanta mana, yanasa lalacewar mahaifa, kuma yanasa cutukan gabobi, Wannan wajibine anisanceshi.

Tsarin iyalin da musulunci yayarda dashi shi ne wanda lalura tasa dole mace tadaina haihuwa, kodai saboda siranta kwan-kwasonta ba ta iya haihuwa dakanta, ko saboda wata cuta datasa dole tayi tsarin bisa sharudda biyun can da muka ambata.

Amma irin wanda yahudawa da 'yan bokoko suke tallatawa mutane wai ka ƙayyade iyalinka daka mace ɗaya ko 'ya'a uku zuwa biyar wannan haramunne yahudancine wajibine musulmai sutashi suyaƙi wannan bala'in.

Babu inda yahalatta haka kawai saboda yahudanci ma'aurata su dena haihuwa wannan ba musulunci ba ne.

Insuna so sudunga samun tazara daka haihuwa zuwa wata haihuwar Saisubi tsarin musulunci wajan Yaye yaro kada suke yaye yaro sai ya cika shekara biyu kamar yanda alƙur'ani yabasu shawara.

Sudunga yin azalu ko mula masa inzasu biya buƙatar sha'awarsu dan kada ciki yashiga wannan shi ne tsarin iyalin da musulmai zasu iya yi amatsayin tazarar haihuwa, ba irin wanda makiya Allah yahudawa suke fesa gubarsa cikin al'ummar musulmai ba, bisa da'awar hakan nakawo talauci da yunwa, Allah yayi mana tsari daka makircin kafirai yahudawa.

mijinda bayasan haihuwa saboda tsoran dawainiyar 'ya'ya kibi duk hanyar data kamata kinuna masa addinin musulunci baiyarda da hakanba, kuma ke yana cutar dake dan kinasan haihuwa, inkikayi iya ƙoƙarinki yaƙi, ki kabi duk hanyoyin daya kamata babu wani canji toki nemi yasakeki kawai babu Alkhairi atare da shi wannan mijin.

Bakiyi laifi ba idan kika nemi yasakeki anan, kinemi kodai yahakura kuci gaba da hayayyafa koya sakeki danke bazaki iya zama dashi ba.

Kuma aibashi ne zai azurtasu ba, Allah ne, kinuna masa shi sunawane agidansu ubansa shi kaɗai ko su biyu yahaifa amma ya akayi yanzu kowa yana rayuwa iya wacce Allah yaƙaddara masa na arzikinsa!!

Arzikinsu ba'a hannunsa yakeba aikinsa yayi tarbiyyarsu yadorasu a kan hanya taƙwarai, shiriyarsu da arzikinsu yana hannun Allah wanda shi ne ya'azurta kafiri da zindiƙi dajahilin dan bokon da turawa suka jirkita masa kwakwalwa.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments