Hukuncin Matar Da Take Zina A Shinfidar Mijinta

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam barka da safiya ya ƙoƙari ALLAH ya bada lada malam Dan ALLAH miye hukuncin matar auren data kawo wani namiji a gidan mijinta ya tattabata Kuma Meya kamata Wanda ya aikata wannan zunubin yayi Dan tsira da azabar ubangijinshi? ALLAH ya baka ikon ansaman tambayata ngd.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

    Tabbas Wannan Mata Ta ci Amanar Allah da Manzonsa Sannan Taci Amanar Aure, Haka Zalika Taci Amanar Mijinta. a kan Haka Kuma Akwai sakayya tsakaninta da Mijinta. Sannan Kuma ya Kamata ta sani cewar Wallahi duk matar Auren da take yin Zina ko irin wannan Iskancin da wani Namiji daban. Wanda ba Mijinta Ba. Wallahi ba ta Yin Lasting, Ma'ana Da gaggawa Allah yake Tona Mata Asiri. Dalili Shi ne, wani ne fa ya Aureta, don ya kare Mutuncin Kansa da Mutuncin Duk Abin da zaizo duniya ta Tsatsonsa. Amma ita ba ta kare Masa kanta ba. Sai Taci Amanar sa.? Subhanallah...

     Sakamakon Wani ya Aureta don ya Kare kansa daga Fadawa Tarkon Shaiɗan. Sakamakon taruwa da mutane Sukayi, A bisa Sharadi Na Aurenta da wannan Bawan Allah. Sakamakon Mutane da suka Haɗu a mazaunin shedun Aurenta da wannan bawan Allah ɗin. Wallahi Allah ba zai bari wannan Shirman Nata ya tafi a Banza ba.

    Sabida haka Abin da yake kanta na Wajibi Shi ne, ta kare masa hakkinsa na Auratayya. Sannan ta kare masa Mutucinsa. Idan ba ta son shi ta Fito ta gaya Masa Mana ya sake ta. Amma wannan cin Amana har ina.? Tsabar Wani Kwarin Rai, Harda kawo Namiji har Cikin Ɗakin da Mijinki yake Tarawa da ke Kuna yin Fasikanci? Wannan Rashin Kunya da Rashin Ladabi da yawa yake. Subhanallah...

    Sannan Shi wanne irin Maras Tunani ne zai Biki Har Gidan Mijinki? Wanne irin Jarababbe ne Shi?

    Hakika laifi ne babba ga Musulmi yaje ya'aikata zina, Shin yanada da aure ko bashida aure haramun ne agareshi yayi Zina, domin Zina tana daga cikin manyan laifuka da Allah() ya haramta a kan dukkan musulmi namiji ko mace, Kamar yadda Allah() yake cewa a Suratul isra'i Aya 32

    وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا

    FASSARA:

    Allah() ya ce: kada ku kusanci zina, domin ita alfahashace dakuma mummunar hanya

    Saboda Mugun laifin dake cikin zina, shi yasa Allah ya tanadar da hukuncin Jefewa ga Mazinaci ko Mazinaciya in dai sun taɓa yin aure. Idan kuma Samari ne ko 'yan mata ana yi musu bulala ɗari-ɗari ne mutukar dai laifin ya tabbata akansu.

     Maganar gaskiya Wannan Mata ba ta kyauta ba. Kuma ina Umartar ta da taji Tsoron Allah ta dena. Tayi tuba Na gaske. Irin Tuban da ba zata sake komawa aikata wannan Abin da ta Aikata a baya ba.

     A haka ne Mutum yake zuwa Asibiti idan an gwada jininsa sai Likita Ya Tabbatar Masa da Cewar yana ɗauke da Cutar HIV. Zaka Samu Matarsa ta Dakko ta goga masa. Sabida shi Mazinaci ba ruwansa da wannan Jinyar. Asali ma Gani yake kamar babu ita. Shiyasa kowacce Irin Mace Ya samu. Baya Tunanin Faruwar Komai, dan da nan indai Har ta Bashi Hadin Kai Zai Afka Mata. Sai ya dakko Jinya a wani wuri a haka Kuma zai yi ta Yadawa tsakanin Mutane.

    Allah ya sawwake Mana. Ya kare Mana 'yayanmu da Matanmu da Mazajenmu. Allah ya Bamu Tarbiyya ta Gari.

    Allah Shi ne Masani.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

    HUKUNCIN MATAR DA TAKEYIN ZINA A SHINFIDAR MIJINTA

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamualaikum malam. Ga tambayata Malam dan Allah menene hukuncin matar auran da takeyin zina Kuma a shimfidar da suke kwana da mijinta? Dan Allah malam adaure abani amsa domin wata qawatace. Kuma Wallahi Tana cikin dana-sani da nadama. Kuma yawanci tacemin harga Allah mijinta ne yake jefata acikin wannan halin. Domin baya Kashe Mata matsalar gabanta. Ma'ana Koda hidima ta taso mata to baya ko sauraranta balle ko kwatatta Mata wani abun yi Kamar irrin sha'nin gidansu ko sha'nin kawaye malam kasan Ana anko Amma Koda ankon gidansu baya mata Kuma Koda kwandalah. Bebata yace takai tace gudummawar Tani hakan baya Mata Daɗi. Shiyasa takeyin haka Amma tacemin inSha Allahu tayi nadama bazata sakeba. Shine nace dan Allah malam ataimaka. Aganar da ita abinda zatayi Allah ya gafarta Mata. Ma assalam ngd malam.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    Wannan Iskanci ne gaskiya. Ba ta da wata Hujja Kwakwkwara da zata kai ta ga Aikawa Zina. Kawai dai Yar Iska ce. Kuma ta ji Tsoron Haɗuwarta da Ubangiji. Dan ma ta ce ta dena.

    Akan wani Anko ne Zatayi Zina. Ankon dole ne.? idan ba tayi Anko ba Auren ba zai yiwu ba ko yaya? Dole ne sai ya bata kuɗin da za tana kaiwa Kawayenta.? Ina Ruwansa da kawayenta.? Kawai dai Yar Iska Ce.

    Idan matar aure tayi Zina, hakika ta aikata babban Alkaba'ir. Domin hakika in banda shirka babu wani laifi mafi girma kamar zina. Shi yasa ma Allah yace kada bayinsa muminai su kusanceta. Saboda Mugun laifin dake cikin zina, shi yasa Allah ya tanadar da hukuncin Jefewa ga Mazinaci ko Mazinaciya in dai sun taɓa yin aure. Idan kuma Samari ne ko 'yan mata ana yi musu bulala ɗari-ɗari ne mutukar dai laifin ya tabbata akansu.

    Allah ya shiryar da Mu Gabaki ɗaya.

    Allah shine Masani

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.