Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi Rahama Ne Ko Azaba? (Fitowa Ta 41)

3) Ya zama dole ga mace ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta mallaki kanta a duk lokacin da kishinta ya taso wanda ake fassara shi da bacin rai. Wannan ma wani babban mataki ne da in ta dauka lallai za ta magance baƙin kishi nan gaba. Tabbas wasu lokatan da za ta riƙa ganin abubuwan da ranta bai kwanta da su ba, kar ta yi ƙoƙarin daukar mataki a lokacin da ta sami kanta a haka, ta bari tukun har sai ta tabbatar da abin da take zargi, koda ma ta tabbatar din ta lissafa: Shin ya dace ta yi wani abu a kai yanzu ko sai nan gaba?

Wasu lokutan shurunnan magani ne, kuma banban makami ne dake taimakawa wurin yaƙin abubuwan dake damun mace a cikin gida. Wani ya zo wajen Annabi SAW yana neman ya yi masa fada. Sai Annabi SAW ya ce "Kar ka yi fushi" yana ganin ya riƙe wannan za a iya ƙara masa, amma Annabi SAW ya yi ta maimaita amsa daya duk lokacin da ya maimaita tambayar. Fushi shi ne asalin abin da ke sanya mace yin nadama a rayuwar aurenta, in ba ta fusata ba ba za ta iya zartar da komai na kishi ba, dalilinsa take jefa maganganu, sai da shi take iya raba wani da ransa, in kuwa aka kai wannan matsayin to me ya rage?

Duk abin da mace za ta gani wurin abokiyar zamanta, ko wurin mijinta wanda zai iya bata mata rai to ta daure ta kawar da kai. Bisa wannan dalili ne lokacin da Annabi SAW yake sifanta jarumi ya ce "Mai zubar da mutane a ƙasa ba shi ne jarumi ba, jarumi shi ne mai iya mallakar kansa lokacin da ransa ya baci" banda ba cewar hankali me zai sa mace ta fito tsirara a gaban jama'a don dai kawai ta hana maigidanta ƙarin aure ko ta sa ya sake ta? Wani zai ga abin kamar tatsuniya amma wallahi ya faru.

Ita a ganinta babban abin da za ta yi masa ke nan ya sa ta kai ga burinta. Sai hankalinta ya dawo jikinta komai ya kwaranye sannan ta fara jin kunyar hada ido da abokan, amma me ya hana ta ji kunyarsu a wancan lokacin? Ni a ganina ma wannan da sauƙi ga maigidan, ba kamar wace ta bari sai da maigidanta ya zauna a majalisarsu ta kasuwa sannan ta ratso ciki ta yi damara ta ci kwalarsa, ta hada masa da zagi kana tana cewa in ya isa da haifaffe a cikin uwarsa ya ba ta takardarta a nan take. In ya dake ta ya zama mai dukan mata har a kasuwa, ya sake ta a ga rauninsa, ya ƙyale ta kuma ya zama abin magana.

Da suka dawo gida ya yi mata abin da ta buƙata sai kuma ta dawo tana bin hanyoyin da zai koma da ita. Har kasuwa fa! To ko a cikin dakinta ne matuƙar maganganun da za ta gaya masa za su sosa masa rai har a kai ga saki me zai hana ta mallaki kanta ta zabi kalmomin da za ta yi amfani da su? Na ga macen da sakinta aka yi amma kowa sai barka yake mata duk da cewa hankalinta a tashe ne tana son mijinta, soyayyar ta riga ta rufe mata ido ba ta ganin komai, sai ma daga baya da ta dawo hayacinta ta tsane shi, ya sha wahala, sai da ya yi kamar zai haukace.

To ta fi shi gaskiya, ga shinan tun ba a je ko'ina ba har uwar nune ta nuna. Da a ce ya iya mallakar zuciyarsa kafin ya sake ta ƙila da bai yi nadama ba. In mace na son ta rabu da baƙin kishi to ta yi ƙoƙarin ganin ta sifantu da dabi'u masu kyau, hakan zai hana ta abkawa kogin nadama, don galibin abubuwan da baƙin kishi ke haifarwa da wahala ka ga an sami na yabo a ciki koda kuwa ƙwara daya ne. Ka sake duba su za ka ga a cikinsu akwai rashin imani, inda mace za ta yi ƙoƙarin kashe kishiyarta saboda namijin da zai iya sakinta ya kore ta a gidansa. Wannan a duniya ke nan fa, wace ta yi kisa ai ta shiga uku a lahira, don ba ta ba rahamar Allah, an fadi hukuncin wanda ya yi kisankai bisa son zuciya.

Sakamakon haka ne wata ta yi ƙoƙarin kashe kishiyarta aka sami akasi a wurin zartar da tsafin, sai roƙon mijin da 'yan uwansa take su yafe mata za ta mutu, kamar wasa kuwa sai da ta bar duniyar, bokan ne ya tona maganar da ya zo wurin. Wani irin baƙin kishi ne haka da yake kaiwa ga kisa? Me take so ta samu a duniya wanda kishiyar za ta hana ta? Galibin masu ƙoƙarin yin kisannan ba su ne suke shan wahalar auren ba wanda suke wahalarwa ne, hakan kan faru ne a lokacin da suke ƙoƙarin mayar da komai nasu su kadai.

Sai kuma rashin tausayi, shi ne ma ya fi yawa, inda wata za ta haukatar da kishiyarta don dai ta zauna daga ita sai mijin a tsakar gida, wace aka haukatar kuma ko me za ta zama wannan ita ta sani. Har gwara ma wace za a yi ƙoƙarin ganin an raba ta da mijin ta hanyar makirci ko tsafi ko sharri. Duk wace za ta yi wa kishiya tsafi za ka taras ko dai hankalin maigidan na kan kishiyar ko hankalintabna kansa, wannan kuma ba ta son haka, don haka yanzu burinta kawai ta raba su. Amma da da gaske ne kishi ke kawo so meye na ƙin wanda yake matuƙar son masoyinka?

A Nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments