Ambaton Allah yana raya gidaje Annabi (ﷺ) ya ce: “Misalin gidan da ake ambaton Allah a cikinsa da gidan da ba a ambaton Allah a cikinsa, kamar misalin rayayye ne da matacce.”
Ayoyi da dama
da kuma Sunnar Annabi (ﷺ)
suna karfafa mana tare da ingiza mu zuwa ga yin zikiri da ambato da tuna Allah.
Kuma suna umartar mu a kan yin zikirin da yawa tare da yi mana bayanin irin
ladaddakin da masu yawaita zikiri suke samu a cikin ayoyi masu yawa da hadisai
da dama.
Allah
Madaukaki Yana cewa:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ
آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا
(“Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ambaci
Allah, ambato mai yawa.)
وَسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا
Kuma ku tsarkake Shi a safiya da maraice.
هُوَ الَّذِي يُصَلِّي
عَلَيْكُمْ وَمَلَائِكَتُهُ
Allah Shi ne
Wanda Yake yi muku salati (tsarkake ku) da mala’ikunSa (su ma suna yi muku
addu’a)
لِيُخْرِجَكُم مِّنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ
domin Allah Ya
fitar da ku daga duffai (na kafirci da gafala) zuwa ga haske (na imani da
tsarkaka).
وَكَانَ بِالْمُؤْمِنِينَ رَحِيمًا
Kuma Allah Ya kasance Mai jin kai ga muminai.”
Ibn Abbas (RA)
ya ce: “Idan kuka aikata haka – ma’ana kuka yawaita zikiri ko ambaton Allah
Madaukaki – Sai Allah Ya yi muku salati (addu’a, Shi) da mala’ikunSa.”
Kuma Allah
Madaukaki Ya sake cewa:
وَالذَّاكِرِينَ
اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا
(“Masu ambaton
Allah da yawa maza da masu ambaton Allah da yawa mata, Allah Ya yi musu
tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma.”)
Kuma Ya sake
cewa:
وَاذْكُرُوا
اللَّهَ كَثِيرًا لَّعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
(“Kuma ku
ambaci Allah da yawa, tabbas za ku samu nasara.”) Da sauran ayoyi da hadisai
masu yawa da suke kwadaitarwa da karfafa Musulmi su yawaita ambaton Allah kuma
suke umartarsu da ambatonSa da yawa.
Ina roƙon
Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai
iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji
na Alƙur’ani
ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai
الله تعالى أعلم
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ
ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ
ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
****************************
Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************
Telegram
https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx
WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.