Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi Rahama Ne Ko Azaba? (Fitowa Ta 40)

2) Dole ko kina so ko ba ki so ki guji bibiyar maigidanki a boye da zahiri in kina son zama lafiya, domin ko kin sami abin da kike bincikawar ba abin da za ki iya yi a kai sai dai ki zada wa kanki da hankali. Wasu matattarun da suka ci gaba ciki har da waɗanda suka auri 'yan boko a matattarunmu za ka taras matan kan riƙa bibiyar mazan don ganin abubuwan da suke sakawa a stories dinsu na fesbuk ko status na WhatsApp da sauran groups da pages don ganin wa mazansu za su yi magana da su, me kawo hakan?

Duk wani post da maigida zai yi ko comments sai matar ta karanta, in ma yana magana da wata sai ta bi ta don tabbatar da cewa ba ta da wata alaƙa da maigidanta. In har ta same su suna tattauna wani batu ko ya yake to dayan biyu ne, ko dai shi maigidan ya amsa dalili ko kuwa ita wancan ta gani a ƙwaryar cin abincinta. Wannan fa tana sane da cewa kafar sadarwa wata duniya ce dake hada budaddun alaƙoƙi tsakanin mutane, ita da wahala ta fahimci maganar a haka, kawai suna soyayya ne wanda hakan cin amana ne ita kuma ba za ta lamunta ba.

Ko ba a fada ba kishi ne ke jawo hakan. Wasu matan ba haka suke ba, za ka taras da wata koda mijin zai bar waya a bude ya ajiye ta a gabanta ya shiga wanka ba za ta taba kallon inda take ba bare ta kai ga dauka ko ta bincika abin da zai jawo mata tashin hankali. In zan tuna akwai wani mutum da yake neman aure amaryar ta ce ba za a ci gaba ba sai ya gaya wa matarsa. Ta yi haka ne don sanin bala'in matan kuma tana so ta ga yadda zai riƙa warware matsaloli masu girma in sun taso masa.

Gogan ya dawo gida ya rasa ta yadda zai fito mata, yana son ya gaya mata amma yana jin tsoron abin da zai biyo baya, a ƙarshe sai wata hikima ta fado masa. Ya dauko wayarsa ya budo tattaunawarsa da amaryar a kan WhatsApp inda suka tattauna maganar aurensu ya bar wayar a kan teburi ya shiga wanka, yana yi yana leƙowa a sace, sai da ya tabbatar ta dauki wayar ta karanta. Abin da yake buƙata ke nan kuwa, yana shigowa ta haukace masa, amma kuma saƙon da yake son turawa ya isa.

Galibin rabe-raben aure da ake samu a tsakankanin matattarar Turawa da Larabawa za ka taras binciken kafofin sadarwa ko waya da ma'aurata ke yi suke haifar da su. Tunda mutum zai ga abin da ake boye masa ko wanda ake so ya gani, kuma da wahala hakan ta zama aikhairi, tunda za a daga murya wani sa'in a kai ga yaji ko rabuwar aure. Ke nan matakin da ya fi kowanne kyau a nan shi ne nisantar tashin hankalin gaba daya, mace na da sanin cewa in namiji ya yi niyyar ƙarin aure ta waya ba sai a gabanta ba, sai yayyafa wa kanta ruwan sanyi ta huta.

Don galibin maza na magana da 'yanmatansu na kafofin sadarwa a waje ne, ke ma ba ki san an yi ba, ina tabbatar miki ba za ki sani ba tunda ba za a yi a gaban naki ba. Abin da babu ƙarya a ciki waya na daya daga cikin hanyoyin da ake hada aure da su, kusan babu hanyar dake da ƙarfi ma yanzu kamarta, amma a zatonki duk lokacin da maigidanki zai kwashe a waje ba su ishe shi ba sai ya dawo gabanki? Da kamar wuya.

Koda yake in aka samo wata ta hanyar kafofin sadarwar da ta ga wasu abubuwan za ta ji a jikinta cewa akwai abubuwan dake faruwa, za ta aza cewa tabbas wannan take-taken nasa wata yake so ya ƙaro. In kin ga za ki iya hanawa sai ki yi wa tukkar hanci, in ba za ki iya ba kau da kanki ki huta. Kina da damar da za ki tuhume shi in kin ga abubuwan da ranki bai natsu da su ba amma ke matarsa ce, kuma yana da damar da zai ƙaro wasu matan ta kafofin sadarwa ko ta zahiri.

Bare yanzu an sauƙaƙe abubuwa da dama tunda kafofin tattaunawan sun yawaita, maza na da cikakken lokacin da za su tattauna da mace kafin kafin su dawo gida, na ga mazan da suke maida sunan 'yan-matansu na maza, a nan ta ya uwargida za ta gane a kallo daya? Ba wani abu na tayar da hankali a ci gaba da gasa kawai. Kai kuma yallaboi tunda ka san waya a wasu lokutan kishiyoyin matan ne sai ka dauki matakin magancewa, ka guji duk abubuwan da za su tayar da zaune tsaye.

A nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba

 **************************

Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments