Ticker

6/recent/ticker-posts

Budurwata Maƙaryaciya Ce

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslam alaikum. Malam Allah ya saka bisa irin taimakon da kukeyi mana akoda yaushe. Allah ya jikan mahaifa. Ameen. Malam neman shawara nake nema gareka. Malam wacce nake sonta da Aure na ke yawan samunta da yi min karya. Kuma malam inayin iyaka bakin ƙoƙarina wajen janyo hankalinta a kan illan karya da makamancin hakan. Domin irin posting din da kake yi a kan hakan ina yawan nuna mata illar hakan, amma har yanzu Allah bai sa ta daina ba. Malam ni kuma ina kaunarta, domin ina shirin tura iyaye na gidansu nema.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikas salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Hakika Ƙarya tana daga cikin Manyan zunubai (Alkaba'ir) kuma ita ce tushen mafiya yawan miyagun laifuka. Domin hakika malaman tarbiyyah suna ganin cewar mutukar mutum ya siffantu da Ƙarya, to zai iya aikata kowanne irin laifi ma.

Manzon Allah ya ce: "KU GUJI YIN ƘARYA DOMIN ITA TANA KAIWA ZUWA GA FAJIRCI (BUSHEWAR ZUCIYA) SHI KUMA FAJIRCI YANA KAIWA ZUWA GA WUTA. KUMA MUTUM BAZAI GUSHE YANA YIN ƘARYA KUMA YANA SON YIN ƘARYA BA, FACHE SAI AN RUBUTASHI AGUN ALLAH CEWA LALLAI SHI MAKARYACI NE".

shawara da zan baka ita ce: ka cigaba da yi mata wa'azi ako yaushe tare da ba ta shawara a kan Ƙawayen da take yawo dasu. Watakila ko tana ganin irin wannan halayen daga garesu ne.

Kayi ƙoƙari ka rabata da wannan mugun halin amatsayinta na wacce nan gaba kake sa ran zata zamanto uwar 'ya'yanka, kuma malamar farko garesu wacce ita zata ba su tarbiyyah.

Wajen zabar matar aure, Manzon Allah ya bamu shawara muhimmiya ya ce: "LALLAI KU AURI MA'ABOCIYAR ADDINI".

Malamai suka ce Ma'anar Ma'abociyar addini ana nufin mace mai tarbiyyar, mai kyawun halaye kamar haƙuri, kunya, gaskiya, rikon amana, girmama manya, etc.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers 

Post a Comment

0 Comments