Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Dake Fita Ba Tare Da Izinin Mijinta Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mene ne hukuncin macen da take yawan fita agidan mijinta koda saninsa ko bada saninsa ba? Mene ne kuma dalilai daze sa mace tafita agidan bissa karantawar sunnar Annabi (S.A.W) ? Wassalam

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Haramun ne ga Mace ta fita gidan ta ba tare da izinin Mijin ta ba. Yin haka babban kuskure ne ga shari'ar Allah. Duk matar dake fita ba tare da izinin mijinta ba, fushin Allah yana samunta har sai ta dawo ta nemi yafewarsa. Allah ya haramta fita waje ga Mata waɗanda aka yiwa sakin kome (saki 1 ko 2) ballantana waɗanda suke matan aure ne ba'a sake su ba. Allah maɗaukakin sarki Yana cewa a Suratul Ɗalaaƙ aya ta 1:

ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲُّ ﺇِﺫَﺍ ﻃَﻠَّﻘْﺘُﻢُ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎﺀَ ﻓَﻄَﻠِّﻘُﻮﻫُﻦَّ ﻟِﻌِﺪَّﺗِﻬِﻦَّ ﻭَﺃَﺣْﺼُﻮﺍ ﺍﻟْﻌِﺪَّﺓَ ۖ ﻭَﺍﺗَّﻘُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺭَﺑَّﻜُﻢْ ۖ ﻟَﺎ ﺗُﺨْﺮِﺟُﻮﻫُﻦَّ ﻣِﻦْ ﺑُﻴُﻮﺗِﻬِﻦَّ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺨْﺮُﺟْﻦَ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻥْ ﻳَﺄْﺗِﻴﻦَ ﺑِﻔَﺎﺣِﺸَﺔٍ ﻣُﺒَﻴِّﻨَﺔٍ ﻭَﺗِﻠْﻚَ ﺣُﺪُﻭﺩُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ۚ ﻭَﻣَﻦْ ﻳَﺘَﻌَﺪَّ ﺣُﺪُﻭﺩَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﻘَﺪْ ﻇَﻠَﻢَ ﻧَﻔْﺴَﻪُ ۚ ﻟَﺎ ﺗَﺪْﺭِﻱ ﻟَﻌَﻞَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻳُﺤْﺪِﺙُ ﺑَﻌْﺪَ ﺫَٰﻟِﻚَ ﺃَﻣْﺮًﺍ.

FASSARA:

Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã saiku sake su ga iddarsu, kuma Ku ƙididdige iddar. Kuma kubi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada Ku fitar dasu daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãsha bayyananna. Kuma wadancan iyãkõkin Allah ne. Kuma Wanda ya Ketare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Baka sani ba dammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bayan haka.

Manzon Allah Yana cewa: Na horeku da yin adalci wa matanku, domin cewa su Fursunoni ne agareku. Saboda haka mace kamar baiwa ce ko yar fursuna ga mijinta, kuma bazata fita gidansa ba saida izinin sa. Koda Mahaifinta ko Mamanta ko wani na daban sun umarce ta da aikata hakan a bisa ra'ayin jumhurin malamai.

(Al-Fataawa Al-Kubra, 3/148).

Ibn Muflih al-Hanbali ya ce: Haramun ne ga mace ta fita wajen gidan mijinta ba tare da izininsa ba, sai fa a yanayi na larura ko wajibcin shara'ah. (Al-Adaab Al-Shar’iyyah, 3/375)

Imamul Ƙurtubiy ya ce "idan har buƙata ta sanya za a fita ɗin, to lallai ne fitar ta kasance cikin kulawa tare da cikakken suturce jiki"

DAGA CIKIN MANYAN DALILAN DA ZASU IYA JAWO FITAR MACE DAGA GIDAN MIJINTA AKWAI:

1. NEMAN ILIMIN ADDINI: idan har mijinta bashi da ilimin da zai koya mata ibadah, kuma ba zai iya dauko wata macen da zata koyar da ita a gida ba, Kuma shi kansa bashi da malamin da zai koyar dashi sannan ya dawo ya koyar da iyalinsa da kansa.

Kuma wajibi ne koyon ilimi ya zamanto awajen mace 'yar'uwarta zata koya. Idan kuma duk garin babu matar dake da ilimin da zata koya awajenta, shike nan sai mataye da yawa su taru awaje ɗaya sannan a nemo namiji mai ilimi, mai tsoron Allah wanda zai karantar dasu ba tare da sun gan shi ko shi ya gansu ba. (wato a sanya labule atsakaninshi dasu).

2. NEMAN LAFIYA: Idan ba ta da lafiya ya halatta ta fita zuwa asibiti domin ganin likita.

3. ZUMUNCI: Ya halatta ta rika zuwa tana gaida mahaifanta ko makusantanta (kamar Ƙannai ko yayun iyayenta) idan buƙatar hakan ta taso. Wannan ya haɗa har da ta'aziyyah da duba marar lafiya.

4. BAYAR DA SHAIDA: Idan wani abu ya faru wanda ake buƙatar matar taje ta bayar da shaida a gaban alkali ko wata hukuma.

5. SANA'A: Ya halatta ta fita taje tayi sana'a idan har mijinta ba zai iya ɗaukar nauyinta ba, Kuma ba ta da wani wanda zai taimaka mata. Amma wajibi ne sana'ar ta zamto halastacciya kuma babu cudanya ko keɓancewa da mazaje acikinta.

6. FITA DOMIN HALARTAR SALLAH: Yana zama halal idan har zasu fita bisa cikakken lullubi tare da rashin keɓancewa ko cuɗanya da maza. Ya halatta su halarci sallar Eidi ko Jumu'ah, har sallolin farilla a masallaci amma akwai Ƙarin wasu Ƙa'idodi da malamai suka ajiye.

Amma fita don yin cefane ko kaiwa yara makaranta, wannan hakkin namiji ne. Bai halasta mace ta fita musamman domin yinsu ba, sai dai bisa larurar rashin miji, ko wani Muharrami wanda zai isar mata.

WALLAHU A'ALAM

Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments