Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Take Yiwa Mijinta Karya Idan Zata Fita

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum dafatan kuna lafiya malam ina da tambaya. wata matace malam zataje gidan rasuwa daga anguwansu to bayan taje ta dawo se da mijinta yadawo setace masa ai batajeba se gobe shi kuma seya sake barinta taje kawai wai tanaso ta haɗu da yan'uwanta a gidansu to malam ya hukuncinta yake Allah yasa mudace.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam:- Ta yi Karya Ko Kuma in ce ta Zama Makaryaciya, Kuma wannan Cin Amanar Miji ne Yaudara ce wannan, kuma Ɗaya daga Cikin Siffar Munafukai ke nan, Shi ne Yin Karya.

Annabi muhammad ya ce Bone wato Narkon Azaba ta Tabbata ga masu Kirkiro Karya. Annabi Sai da ya maimaita wannan Kalmar har sau 3. Ina za ki sa kanki a Ranar Alkiyama da kullum kike yiwa Mijin Ki Karya Don biyar Buƙatar ki?

Sa'annan wannan Cin Amana Ne, Kuma Duk Mai Cin Amana Bai Ketare Gadan SIRADI, domin Sai Amana ta zo ta tsaya a Gefen Gadan SIRADI, ta ba da shaidar Cewa ba ki Ci ta ba tukuna kafin za ki wuce. Mijin ki ya yarda da ke ya ba ki Amanar Fita zuwa inda Kika Tambaye shi, Kika fita Kuma Kika je inda Kika tambaya, Kuma Kika dawo Wai ki ce Masa ke ba ki je Wai Sai gobe za ki je. Kin Yaudare shi Kuma Kin Ci Amanar sa.

Sa'annan inda za ki je ba tare da Izinin sa ba, har ki je ki dawo kina tare da Tsinuwar Allah da na Mala'ikun sa. Wacce irin Rayuwar ce wannan? Da ke ba za kiyi gaskiya ba Wai sai kin haɗa da Karya? Kin San illar yin karya ma kuwa? Kina musulma? Kuma Haihuwa kike Yi? Idan Ɗiyar ki ta koyi hakan Anya kin San wanne illa za ki Jawo mata kuwa? Ko Kuma idan Yaran ki su koyi Karya Kin San wanne Hali za ki je fa su kuwa? Meyasa Ku mata kuke jefa kanku Cikin Hallaka ne da kanku?

Yanzu idan Mijin ki ya gane Cewa Karya kike Yi Masa, Shin mene ne Matsayin ki a gurin sa? Idan ya gane Cewa Karya kike yiwa Masa kullum ya ce ya Sake ki dalilin hakan, Shin Ina Amfanin Haduwa da Yan Uwan Naki yake? Irin Haka ne wallahi sai Ki ga Mazan ku sun Fara Zargin ku, da Cewa ai kuna zuwa Neman Maza a waje wani ma ya ce ai Zina kike fita kiyi, me amfanin yin karya ga Mijin ki? Ba kiyiwa Mijin ki gaskiya ba toh waye Kuma ya saura Miki? Idan ya gane Cewa Karya kike Masa ai daga wannan Ranar duk Gaskiyar ki wallahi ya Dena yarda da ke kenen ko me kike Yi Kullum Cikin Karya kike da Zargi, Me Kika yiwa Kanki toh? Ku Mata kune kuke jawowa Kanku Masifa da Bala'i wallahi daga karshe ku dawo Wai Kuna Nadama, wannan ai ya Zama Nadamar Banza Ke nan. Ku JI Tsoron Allah Wallahi. Allah Yasa mu dace 🤲

WALLAHU A'ALAM .

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments