Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan Da Ake Iya Fasa Aure Saboda Su

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, da fatan mallamai da dukkan 'yan uwa suntashi lafiya. Ina rokon Mallam bayani kan hukuncin Wanda aka sanyama ranar aure kafin lokacin ya ce ya fasa.

Allah ya karama mallam lafiya da basira. Ameen

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa!alaikum assalam, in har akwai hujjar da sharia ta yadda da ita, ba shi da laifi in ya fasa, kamar ya bayyana budurwar tasa ba tada tarbiyya ko mazinaciya ce, ko kuma ba ta son shi, ko tana da cutar da za ta hana a sadu da ita, kamar toshewar farji ko hadewarsa da dubura, ko ya zama şu duka suna da jinin da in sun haɗu za su haifi sikila, yana iya fasa auren. idan ya zama ba shi da halin da zai iya ciyar da ita, ko kuma likita ya tabbatar maşa ba shi da mazakutar da zai iya saduwa da mace, haka ma idan ya ji ya tsaneta.

Dukkan abin da ake iya saki saboda shi, ana iya fasa aure ın aka same shi, an shar'anta saki ne saboda tunkude cuta daga ma'aurata ko ɗaya daga cikinsu, yana daga cikin ka'idojin sharia da kuma masu hankali: Tunkude cuta kafin ta auku ya fi sauki fiye da ƙoƙarin kautar da ita bayan ta faru.

Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments