Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Auren Da Aka Yi Ma Fyaɗe

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah. Dan Allah malam ina da tambayoyi ne guda uku duk da cewa ta farkon kusan a haɗe suke. Tambaya ta ita ce matar aure ce akayi mata fyaɗe sannan ta cigaba da kwanciyar aure da mijinta. Shin akwai aure a tsakanin su ko babu? kuma zasu iya cigaba da zaman aurensu akan haka? Sannan zata iya faɗa masa ko Kuma a'a, saboda gudun zargi ?

Na biyu Kuma sai ciki ya bayyana a tare da ita Kuma sannan ta cigaba da kwanciyar aure da mijinta shin akwai aure a tsakaninsu ko babu? kuma meye matsayin auren ?

Na uku Kuma shi ne macece a kaima auren dole har Allah yasa ahalin yanzu suna da yara kusan 8 amma tace har yanzu babu digon sonsa a ranta wai zata iyayin karya da wata laluran dan ya saketa wai bazata iya cigaba da rayuwarta dashi ba. Nagode sosai Allah biyaka da mafificin Alkhairi duniya da lahira amiin ya hayyu ya qayyum.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullah.

Hukuncin matar da aka yiwa fyaɗe shi ne: dole ne ta sanar da mijinta saboda hakkinsa na aure. Sannan kuma wajibi ne tayi zaman istibra'i wato domin tabbatar da ko ciki ya shiga ko bai shiga ba.

Zata zauna tsawon lokacin da za ta yi haila. Idan hailarta tazo koda sau ɗaya ne, to shikenan ta samu tabbacin cewar ciki bai shigeta awannan fyaɗen da akayi mata ba.  Amma idan har ciki ya shiga, babu damar mijinta ya kwanta da ita sai bayan ta haife abin da ke cikinta. Domin Manzon Allah ya hana mutum ya shayar da shukar da ba tasa ba.

Bayan ta haife cikin kuma sai ta cigaba da zaman aurenta da mijinta. Domin wannan fyaɗen bai lalata aurensu ba.

Amma yanzu tun da har ta cigaba da mu'amalar auratayya da mijinta, dole wannan abin da ta haifa ɗin ya zamto na mijinta ne. Tun da Manzon Allah yace "YARO NA SHIMFIDA NE" (wato mamallakin shimfidar shi ne mamallakin yaron).

Matar da aka yiwa auren dole tana da damar neman yin khul'i da mijinta. Wato ta biyashi sadakinsa shi kuma ya saketa. Amma neman sakin aure ba tare da wani kakkarfan dalili ba, haramun ne.

Hakanan kuma Manzon Allah yayi gargadi mai tsanani game da duk matar da taje tayi zina ta samu ciki sannan ta dangantashi zuwa ga mijinta alhali ta san ba ɗansa bane. Yace ba zata ɗanɗani komai na rahama ba.  Ko kuma Allah bazai dubeta da rahama ba.

Ya zama wajibi mai wannan tambayar kiji tsoron Allah ki rika tunawa da lahirarki. Duk abin da kika aikata anan duniya fa, zaki tarar da sakamakonsa aranar da babu damar yin Qarya, ko kin yi ma bazata rage miki radaɗin azaba ba.

Amatsayinki na matar aure, me ya kaiki har kika keɓance da wani Qato, har yayi miki fyaɗe? Kuma in da gaske fyaɗen akayi miki, me ya hana kiyi eehun sa jama'a zasuji domin su kawo miki 'dauki??  Kuma me yasa baki sanar da mijinki ko danginki don su ɗauki matakin sanar da hukuma don nema miki hakkin cin zarafin da akayi miki ba??

Ki tuba ki nemi yafewar Allah da yafewar mijinki domin hakika kin zalunci kanki kuma kin zalunci mijinki.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments