𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum malam barka da safiya. malam ina cikin wani yanayi shi ne nace bari in
nemi shawara gurinka. Malam ina Shan wuya agidan aurena. Mijina ya kasance baya
ganin darajata da kimata. ba so ko ɗaya. Duk maganar da ta fito bakinsa sai ya fada
min duk zafinta. Wulakanci kala kala. shekara Tara ina zaman hakuri darajar
aure da darajar iyayena. Malam abin kamar an farraka mu. Duk Inda na samu
addu'a don zaman lafiya da soyayya yinta nake. Malam har da addu'o'in karya
sihiri nayi sau dayawa. Mal shi ne aka ban shawara da in yanke faratuna in kona in hada da jinin haila in bashi ya ci
zai daidaita. shi ne nace bari in tambaya shin ya dace inyi hakan. na gode
Allah ya saka.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Baiwar Allah ki sani cewa zamanki agidan Mijinki
zaman ibadah ne. Kuma ita ibadah ga mumini alkhairi ne. Kuma ba lallai ne dole
sai komai ya tafi kamar yadda kike so ba. Dole sai kin yi hakuri da duk halin
da kika tsinci kanki. Shi hakuri abu ne mai lada sosai kuma Mumini yana samun
Qarin lada da daukakar darajoji ta dalilin hakurinsa akan halin da ya tsinci
kansa.
Allah Madaukakin Sarki yace : "KAYI HAKURI
SABODA HUKUNCI UBANGIJINKA.. ". Wata Mata takai Qarar mijinta wajen Manzon
Allah ﷺ akan
halinsa. Sai Manzon Allah ﷺ yace
mata "KI DUBA, MIJIN NAN NAKI SHI NE WUTARKI KUMA SHI NE ALJANNARKI (WATO
IDAN KIN YI HAKURI DASHI KIN YI MASA BIYAYYA ZAKI SAMU ALJANNAH. IDAN KUMA KIKA
SAƁA MASA ZAKI SHIGA WUTA). Ki sani cewa Mijinki duk taurin kansa da
wulakancinsa bai kai Fir'auna ba. Amma ga Matar Fir'auna nan ta shiga Aljannah
saboda dalilin hakurinta da kuma Qardin imaninta. Kada ki biye ma Qawaye da
'Yan uwa Mata masu baki miyagun shawarwari. Hakika zasu sanyaki cikin ramin
shirka ne da tsafe-tsafe irin na kafirci.
Manzon Allah ﷺ yace "BA YA CIKINMU DUK WANDA YAJE
CHAMFI KO KUMA AKAYI MASA CHAMFI, KO YAYI BOKANCI KO AKAYI MASA BOKANCI. KO
YAYI TSAFI KO AKAYI MASA TSAFI DOMINSA. DUK WANDA YAJE WAJEN BOKA KUMA YA YARDA
DA ABIN DA YA GAYA MASA, TO YA KAFIRCE WA ABIN DA AKA SAUKAR WA ANNABI MUHAMMAD
ﷺ (Imamul Bazzar ne ya ruwaitoshi
da isnadu mai kyawu).
Don haka duk wacce taje wajen boka aka bata wani
abu tayi amfani dashi ko kuma ta sayar wa wadansu matan sukayi amfani dashi, to
tabbas gaba dayansu laifin ya shafesu (wato kafirci kamar yadda hadisin ya
bayyana).
Farce da kuma jinin haila duk Qazanta ne. Yadda
kika san ke kanki ba zaki iya ci ba, to bai halatta ki sanya ma mijinki cikin
abincinsa ba. Kuma bayan zaluncin dake cikin yin hakan ga kuma Shirka ne da
champe-champe. Kuma Allah ya hana.
Mata kuji tsoron Allah ku fahimci cewa samun
mallakar zuciyar miji ta hanyar amfani da layoyi ko kulle-kullen tsafi ba samun
yardar Allah bane. Hasali ma hanya ce ta kafirci da gushewar imani. Amma zaku
iya samun mallakar mazajenku ta hanyar ladabi da biyayya da girmama miji tare
da gyaran jiki da kyautata halaye. Kuji tsoron Allah ku tsaya bisa abin da yake
na halal. Wato addu'a da kuma neman mafita awajen Allah. Tare da Qaurace ma bin
miyagun shawarwari irin na bokanci.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYoz
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.