𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Meye matsayn iddar matar da mijinta yasaketa tana
shayarwa, watanta tara amma haryau bataga jini Haila ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله والصلاة والسلام على أشراف الأنبياء والمرسلين، صلى الله عليه وعلى آله وأصحابه وذريته ومن سلك سبيلهم إلى يوم الدين.
Macen da'aka saka, idan mijinta yasaketa kafin
yakebanta da ita yai jima'i kosu rungumi juna da kwanciya da ita, babu iddah
akanta kai tsaye, dazarar yasaketa shikenan yahalatta wani yanemi aurenta suyi
aure batareda ɓata
lokaciba.
Amma idan yasadu da ita jima'i kenan, koya kebanta
da ita tozatai iddah idarta kuma zata kasance tafuskoki kamar haka:
1- idan tanada ciki dazarar tahaihu tagama
iddarta, lokacinda yasaketa tadau lokaci kafinta haihu, ko bata dau wani
lokaciba ta haihu, misali mijinta yasaketa karfe ɗaya na rana karfe biyu ko uku na rana
saita haihu to takammala iddarta, koda tazarar minti ɗaya ne tsakanin sakinta da haihuwarta
tagama iddarta.
Haka dazai saketa awatan muharram bata haihu ba
sai awatan zul-hijjah to haihuwarta ita ce gama iddarta.
Atakaice dai maiciki in aka saketa dazarar tahaihu
tagama iddarta saboda faɗin
Allah maɗaukakinkakin
sarki:
وأُﻭﻻﺕُﺍﻷَﺣْﻤَﺎﻝِ ﺃَﺟَﻠُﻬُﻦَّ ﺃَﻥْ ﻳَﻀَﻌْﻦَ ﺣَﻤْﻠَﻬُﻦَّ
Mace mai ciki iddarta shi ne tasauke abun dake
cikinta.
2- idan kuma batada ciki amma tana haila to
iddarta ita ce jini uku wato saitayi haila sau uku, wata uku kenan, an samu
lokaci maitsawo kafinta tai jini ukun bayan mijinta yasaketa ko ba'a samu
lokaci mai tsawo ba.
Idan miji yasaki mace tana shayarwa amma haila
batazo mataba sai bayan shekara biyu zataita zama har shekara biyu, tana cikin
iddah harsai tai haila sau uku, zata zauna tsawon shekara biyu ko sama dahaka
sannan tai jini uku.
Abu mafi muhimmanci akan iddar mai shayarwa shi ne
saitayi jini uku, tadau tsawon lokaci kafin tai jini ukun ko bata dau lokaci
mai tsawo ba, saboda fadin Allah madaukakin Sarki:
ﻭَﺍﻟْﻤُﻄَﻠَّﻘَﺎﺕُ ﻳَﺘَﺮَﺑَّﺼْﻦَ ﺑِﺄَﻧْﻔُﺴِﻬِﻦَّ ﺛَﻼﺛَﺔَ ﻗُﺮُﻭﺀٍ
Matayenda aka saki zasu zauna cikin iddah tsawon
jini uku, wato sai sunyi haila sau uku.
3- Macenda bata haila imma saboda karamace bata
fara hailaba, ko saboda ta tsufa tadena haila, iddarta shi ne wata uku zatai
tana kammala wata uku tagama iddah, saboda fadin Allah madaukakin Sarki:
ﻭَﺍﻟﻼﺋِﻲ ﻳَﺌِﺴْﻦَ ﻣِﻦَﺍﻟْﻤَﺤِﻴﺾِ ﻣِﻦْ ﻧِﺴَﺎﺋِﻜُﻢْ ﺇِﻥِ ﺍﺭْﺗَﺒْﺘُﻢْ ﻓَﻌِﺪَّﺗُﻬُﻦَّ ﺛَﻼﺛَﺔُ ﺃَﺷْﻬُﺮٍ ﻭَﺍﻟﻼﺋِﻲ ﻟَﻢْ ﻳَﺤِﻀْﻦ
Matayenda suka dena haila iddarsu idan ansakesu shi
ne wata uku, da wadanda basu fara hailarba kobasayi.
4- Wacce tadena haila saboda wani dalili narashin
lafiya daya sameta, kamar wacce mahaifarta ta rufe, itama iddarta wata ukuce
kamar wacce bata fara hailarba, kowacce tadena saboda tsufa.
5- Macen da hailarta tadauke tadena yi kuma ta san
abun da yasa tadena zuwa, malamai sukace zatai iddah tsawon shekara guda, wata
tara na ciki, wata uku na iddah.
wannan shi ne kashe-kashen iddar macenda aka saki.
saboda haka zakici gaba da zama harsai kin yi jini
guda uku, inkuma kun sulhunta mijinki zai iya yi miki kome idan shikan baikai
igiya ta uku ta aurenku ba.
Walalhu A'alamu.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.