Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Girma Alhaji Shehu Umaru ɗan Magatakardan Maradun Ummarua

Mai Girma Alhaji Shehu Umaru ɗan Magatakardan Maradun Ummarua
"Na Macciɗo gamda'aren Sarkin Rwahi ƙi sake,
Mai kasada kamdaren Baraya" i
Inji Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun a cikin Waƙar sa mai amshi "Ɗan Amadu tsayayye, ko ɗauri ba ya wargi" wadda ya yi wa Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar /Hakimin Gundumar Maradun, Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Bello Tambari (ya yi Sarauta daga shekarar 1960 zuwa Shekarar 1980, ya rasu a Shekarar 1985). 
Wannan sh ine Macciɗon da ake danganta sa da shi. Sunansa na yanka shi ne Alhaji Shehu Umaru, ɗan Magatakardan Maradun Ummaru ne, shi ne kuma Magatakardan Sarkin Ƙayan Maradun, Alhaji Muhammadu Bello Tambari, ya rasu a Shekarar 2016. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments