Falalar Ambaton Allah {6}

    Yaku bayin Allah! wajibi ne Musulmi ya san ma’anar kalmar La’ilaha illallahu, kuma ya yi aiki da ita domin tana kore dukan nau’o’in shirka da dukan ababen bauta ta tabbatar da bautar ga Allah Shi kadai. Wajibi ne mutum ya fade ta da harshe kuma ya tabbata ya tsarkake ta a cikin zuciyarsa. Hadisi ya zo daga Abu Huraira (RA) lokacin da ya tambayi Manzon Allah () cewa: “Ya Manzon Allah! Wane ne mafi rabauta da cetonka a Ranar kiyama ? Sai manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya ce, La’ilaha illallahu yana mai tsarkake ta a cikin zuciyarsa.” Ma’ana ba kawai ya fade ta da harshe ba ne a’a har cikin zuciyarsa haka yake nufi. Kuma a wani Hadisin ya ce: “Lallai ne Allah Ya haramta wa wuta wanda ya ce La’ilaha illallah yana mai nufin yardar Allah da haka.” Ba wai ya fadi haka da harshe kawai ba ne, a’a ya kiyaye duk abubuwan da take nufi. Domin lokacin da Annabi () ya ce da mushirikai ku ce “La’ilah illallahu, za ku rabauta.” Saboda sun san ma’ana da manufarta sai suka ce:

    أَجَعَلَ الْآلِهَةَ إِلَٰهًا وَاحِدًا إِنَّ هَٰذَا لَشَيْءٌ عُجَابٌ

    _(“Shin ya sanya gumaka ababen bauta su zama abin bautawa guda ? Lallai wannan hakika wani abu ne ake nufi!”)

    Kuma Allah Ya sake cewa:

    إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ

    (“Lallai su sun kasance idan an ce musu, “La’ilaha illallahu – Babu abin bautawa da gaskiya face Allah,” sai su dora girman kai.”)

    Mutanen Jahiliyya sun ki amincewa su fadi wannan kalma ce, saboda sun san za ta raba su da gumakansu ta ba ta bautarsu ga gumaka su kuma ba su son barin bauta wa gumakansu, sun fi son su ci gaba da rike su.

    Ina roƙon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alƙur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai

    الله تعالى أعلم

    ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​

     ****************************

    Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
    ****************************

    Telegram

    https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx

    WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.

    Sheikh Muhammad Auwal Albany

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.