Ticker

6/recent/ticker-posts

Falalar Ambaton Allah {5}

Yaku bayin Allah! mafi falalar zikiri shi ne fadin La’ilaha illallah, don haka ya kamata kullum harshen Musulmi ya kasance jike da fadin La’ilah illallah. Duk lokacin da mutum ya gafala daga ambaton Allah haƙaƙi imaninsa zaiyi rauni sosai daga nan kuma sai Shaidan ya samu galaba a kansa. Kalmar La’ilaha illallah, kalma ce mai saukin fadi a kan harshe, mai nauyi a wurin Allah.

Ya zo a cikin Hadisi cewa: “Lallai Annabi Musa (AS) ya ce: “Ya Ubangiji! Ka koya min wani abu da zan ambace Ka da shi kuma in roke Ka da shi. Sai Allah Ya ce: “Ya Musa ka ce: “La’ilaha illallah!” Sai Musa ya ce: “Ya Ubangiji! Dukan bayinKa suna fadin wannan.” Allah Ya ce: “Ya Musa! Da sammai bakwai da abin da ke raye a cikinsu koma bayana da kassai bakwai da abin da ke raye a cikinsu koma bayana, za su kasance a kunnen daya na sikeli, kuma La’ilaha illallah, ta kasance a daya kunnen sikelin, to, La’ilaha illallahu za ta rinjaye su!”

Kalmar La’ilaha illallah, kalma ce mai girma, kuma tana da ma’auninta a wurin Allah, ba kalma ce ta lafazi kawai ba, kalma ce mai ma’ana da manufa da wajibi ne Musulmi ya san ma’anar kuma ya yi aiki da manufarta. Ma’anar ita ce: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah – duk wani abin bauta koma bayanSa batacce ne. Da kalmar La’ilaha illallah, aka aiko dukan Manzanni (AS), kamar yadda Allah Ya tabbatar da haka a cikin fadinSa:

وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ

 (“Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabaninka face Muna yin wahayi zuwa gare shi cewa: “Lallai ne shi, babu abin bautawa da gaskiya face Allah sai ku bauta masa”)

Ina roƙon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alƙur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai

الله تعالى أعلم

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​

****************************
Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************

Telegram

https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx

WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.

Sheikh Muhammad Auwal Albany

Post a Comment

0 Comments