Ambaton Allah dai kalmomi ne masu saukin fadi a baki, ba su wahalar da bawa ko su zame masa nauyi, amma kuma suna da lada mai girma da ijara mai yawa. Sannan su kalmomin nan ababen so ne a wurin Allah Madaukaki. Buhari (RA) ya ruwaito a Sahihinsa daga Annabi (ﷺ) cewa lallai shi ya ce: “Kalmomi biyu masu sauki a kan harshe, amma masu nauyi a kan mizani, sannan masu girma a wurin Mai rahama. Su ne: “Subhanallahi wa bihamdihi, subhanallahil azim.”
Sannan zikiri
da ambaton Allah na kore shaidanu daga kusa da bawa, na tsare bawa daga
wasi-wasin shaidanu da sharrukansu da kaidojinsu da duk miyagun tuggunsu. Allah
Madaukaki Ya ce:
وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ
فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
(“Kuma idan
wata fizga ta fizge ka daga Shaidan, to ka nemi tsari daga Allah. Lallai Shi,
Shi ne Mai ji, Masani.”)
Kuma Allah Ya
ce:
وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ هَمَزَاتِ
الشَّيَاطِين / وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن
يَحْضُرُونِ
(“Ka ce:
“Rabbi inni a’uzu bika min hamazatis shayadini. Wa a’azu bika Rabbi an
yahdurun.”)
(Ma’ana: Ya Ubangijina, ina neman tsari da Kai
daga fizge-fizgen shaidanu. Kuma ina neman tsari da Kai, ya Ubangijina! Domin
kada su halarto ni.)”
Kuma Allah Ya sake cewa:
إِنَّ الَّذِينَ اتَّقَوْا إِذَا مَسَّهُمْ طَائِفٌ مِّنَ الشَّيْطَانِ تَذَكَّرُوا فَإِذَا هُم مُّبْصِرُونَ
(“Lallai ne waɗanda suka jin tsoran Allah,
idan wani tashin hankali daga Shaidan ya shafe su, sai su tuna (Allah), sai ga
su sun zama masu basira.”)
Kuma Allah Ya sake cewa:
(وَمَنْ يَعْشُ عَنْ ذِكْرِ الرَّحْمَنِ
نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانًا فَهُوَ
لَهُ قَرِينٌ 36 ) [الزخرف: 36]
(Kuma duk
wanda ya makance ga barin ambaton mai rahama za mu hore masa shaidani sai ya
zama abokinsa).
Kuma Allah
Ta’ala ya ce,
(وَمَنْ أَعْرَضَ عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ
لَهُ مَعِيشَةً ضَنْكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى 124 ) [طه: 124]
(Duk wanda ya
kau da kai ga barin ambaton Allah mai rahama, to yana da rayuwa mai ƙunci,
kuma za mu tashe shi ranar alƙiyama a makaho).
Ina roƙon
Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai
iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji
na Alƙur’ani
ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai
الله تعالى أعلم
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ
ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ
ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
****************************
Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************
Telegram
https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx
WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.