15 - Alamomin tsoron Allah guda biyar ne:
a. Fadin gaskiya
b. Cika alkawari
c. Riƙon amana
d. Jin tausayi da
e. Kyautata ma mutane.
16 - " Rayuwa kamar kasuwa
ce, Ka zagaya ka tsinci duk abin da kake so. Idan ka zo fita za ka biya duk
abin da ka dauka."
17 - " Wanda bai iya karatu
da rubutu ba jahili ne. Amma wanda ya fi shi jahilci shine wanda ya san gabas
amma kuma ba ya sallah. "
18 - Idan ka mutu an rufe
labarinka, amma abubuwa uku suna rayuwa a bayanka :
a. Ilmi da
b. Haifuwar Ɗa
c. Aikin alherin da ka shuka
19 - Abokai iri uku ne:
1 - Mai sonka don abinka.
2 - Da mai sonka don kanka.
3 - Da mai sonka don kansa.
Irin wannan yana tare da kai ne idan ka samu. Idan ka rasa, zai yi ko sama ko ƙasa.
20 - " Idan ka yi fushi ka
kama Bakinka. Domin ba kai ne za ka yi magana ba a lokacin, Shedan ne. "
21 - " Kada ka bar aikin yau
ka ce sai gobe. Gobe ai ta mai rabo ce."
22 - " Kada ka zolayi masu
aikata zunubi. Dukan mu muna cikin suturar Allah SWT ne. Amma ka yi musu Nasiha
da lafazi kyakkyawa. Duk masu laifi ba su kai Fir'auna ba, kuma duk masu wa'azi
ba su kai matsayin Annabi Musa (Alaihis Salam) ba. Amma Allah ya ce da shi :
" Ka gaya ma Fir’auna magana mai laushi, wataƙila zai karvi wa'azi ko ya
ji tsoron Allah SWT. "
23 - " Al'HudaHuda tsuntsu
ne da ya kawo rahoto, ya isar da saƙo, ya nuna kishin addininsa. Kada ka bari
tsuntsu ya fi ka son Allah da kishin addininsa. "
24 - " Abu Jahal cikakken
Balarabe ne, mai kudi, kuma Baƙuraishe. Amma yana wuta. Bilal talaka ne, kuma
Bawa ne, Baƙar fata. Amma yana tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam
a aljanna. Aikin kowa shi yake fisshe shi."
25 - " Idan namiji bai ji
dadin aure ba zai yi tunanin ƙara mata ne don ya samu jin dadi. Idan kuma ya ji
dadi zai yi tunanin ƙarawa don ya ƙara jin dadi. Mata ku yi haƙuri. Ƙarin aure
Dabi'a ce a cikin mazajenku."
26 - " Ba zaka iya yin
hukunci na gaskiya a kan mutum ba, sai idan ba ka da buƙata zuwa gare shi.
Wanda ya miƙa hannu bai miƙe ƙafa. idan Baki ya ci, dole ne ido ya ji kunya.
"
27 - " Maganar gaskiya ba
lalle ne ta zama mai daxi ba, amma tana da kyau da amfani.
28 - " Duk lokacin da
zunubinka ya fara damunka, to ka riga ka kama hanyar tuba."
29 - " Zuciyarka ita ce
adireshinka. Harshenka shi ne ma'auninka. Gyara zuciyarka sannan ka kula da
harshenka. "
30 - " Haƙuri iri biyu ne: " Haƙurin abinda kake so idan ba ka same shi ba, da haƙurin abinda ba ka so idan ya same ka."
Daga Taskar:
Prof. Mansur Ibrahim Sokoto, mni
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.