Ticker

6/recent/ticker-posts

Baran Baji

5.51 Baran Baji

Wannan ma wasan tashe ne na yara maza. Adadin masu gudanarwa na iya kai wa shida ko ma sama da haka. Yana tafiya da waƙa, sannan akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi. Kamar sauran wasannin tashe, an fi gudanar da shi da dare, bayan an sha ruwa.

5.51.1 Kayan Aiki

i. Faifayi

ii. Rariya

iii. Dutsen niƙa (na itace)

iv. Turmi

v. Taɓarya

vi. Tsakiya da munduwar hannu ta mata

vii. Kallabi

viii. Zane

5.51.2Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin masu wasa zai yi shiga irin ta mata. Wannan shi ake kira Baran Baji. Daga nan yara za su tattara kayan aiki kamar yadda aka lissafo su a sama. Yayin da aka je wurin wasa, za a zuba kayan nan wuri ɗaya. Baran Baji kuwa zai nemi wuri ya bararraje ya kama waƙa, saura kuwa su riƙa amsawa. Ga yadda waƙar take:

Baran Baji: Masu gidan nan,

Za ni daka muku,

Za ni niƙa muku,

In tankaɗe muku,

In ba ku gari,

Mai tarin yawa.

Amshi: Haba Baran Baji sauran mai niƙa.

Baran Baji: Na zaga duniya,

Duk na yawata,

Na sha kallo,

Na sha tambaya,

Na sha karo da mutanen duniya.

Amshi: Haba Baran Baji sauran mai niƙa.

5.51.2 Tsokaci

Wannan wasa kwaikwayo ne ko hoto na yadda Bahaushe ke sarrafa hatsi zuwa gari domin dafa abinci. Wani abin burgewa shi ne yadda akan samar da sassaƙaƙƙun kayayyakin da masu tashen ke amfani da su. Ciki har da dutsen niƙa. Sannan waƙar na tabbatar da maganar Bahaushe cewa tafiya mabuɗin ilimi. Tafiye-tafiye a duniya da Baran Baji ya yi, ya samar masa ilimi daban-daban.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments