Ticker

6/recent/ticker-posts

Tashi Mai Kwaɗayi

5.50 Tashi Mai Kwaɗayi

Wannan ma wasan tashe ne na yara maza. Kimanin yara uku zuwa sama da haka ne suke gudanar da shi. Sannan ba ya buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi. Sai dai wasu lokuta ɗaya daga cikin yara na shafe fuskarsa da bula ko wani abu mai kama da wannan. Wannan yaro shi ake kira Mai Kwaɗayi a cikin wasan. Kamar sauran wasannin tashe, an fi gudanar da shi lokacin da aka sha ruwa.

5.50.1 Yadda Ake Wasa

Yara za su zaɓi ɗaya daga cikinsu ya kasance Mai Kwaɗayi. Wani lokaci wannan yaro na shafe fuskarsa kamar yadda aka bayyana a ƙarƙashin 5.50. Yayin da aka je wurin wasa. Mai kwaɗayi zai yi zaman dirshan a ƙasa, ya naɗe ƙafafunsu. Sannan zai riƙa zazzare idanu da tanɗe-tanɗen baki kamar wani maye. Idan aka yi dace sun tarar da wani ko wata nacin abinci a wurin da suka je tashe, abin ya fi armashi. Domin kuwa Mai Kwaɗayi zai zuba wa abincin ido. Sannan har ɗan ja-da-gindi zai riƙa yi yana gusawa kusa da mai cin abincin. Yara za su riƙa masa magana, shi kuwa yana amsawa kamar haka:

Yara: Tashi Mai Kwaɗayi,

Mai Kwaɗayi: Ni ba zan tashi ba sai an ba ni.

 

Yara: Tashi Mai Kwaɗayi,

Mai Kwaɗayi: Ni ba zan tashi ba sai an ba ni.

Haka wasan zai  ci gaba har sai an sallame su.

5.50.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan yana kawo hoton wata rayuwar mai wata ɗabi’a, wato kwaɗayi. An gina wasan kan ban dariya da raha, musamman idan mutum ya dubi yadda mai kwaɗayi ke ta faman lashe baki da zare ido, kamar wanda zai cinye abin da ke gabansa. Ga shi ya yi zaman dirshan sannan allam-fur ya ce sai an ba shi da ya ta shi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments