Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar "Hotona" Ta Mohammed Bala Garba

Waƙar "Hotona" Ta Mohammed Bala Garba

Wannan ne asalin hotona,

 An ɗauke shi ina tashena,

 Kui sebin domin watarana,

 Za ku tunani silar waƙena,

 In na mace ku kira sunana,

 Jikan Garba nake ihiwana,

 Mamman ne asalin sunana,

Ku roƙa min Rabbi Gwanina,

 Don na saɓa masa da rana,

 Har a duhu a cikin barcina,

 Da kuskure sharrin ƙalbina,

 Ya yafe mini don Manzona,

 In ya ƙi ba ni da mai cetona,

 Ku ma na saɓe ku da rana,

Wanda nayo bisa son zucina,

 Ku yafe mini don Manzona,

 In baku yo ba ina zan kwana,

 Na gode bisa jin kukana,

 Kun nuna mini so har ƙauna,

 Ga mutuwa yau ta zo kaina,

 Zan tafi ni kam sai watarana,

 Kui ta'azziya gun Ummina,

 Ku roƙeta ta bar kukana,

 Tai ta du'a'i shi nafi ƙauna,

 Na roƙeku ku zo kabarina,

 Muyi zumunci shi nafi ƙauna,

 Da addu'arku tana doshina,

 Wannan dai shi ne fatana,

 Wanda nake a wajen ihiwana,

 Na gode muku sai watarana.

Mohammed Bala Garba
10 Mayu, 2023.
Sabuntawa
10 Yuli, 2023.

Post a Comment

0 Comments