Ticker

6/recent/ticker-posts

Boka Kake Ko Malami?

8.4 Boka Kake Ko Malami?

Wannan wasa ne da maza yara da manya suke gudanarwa. Yana ɗaya daga cikin wasannin tashe na maza. Adadin masu gudanar da shi na iya kaiwa uku ko sama da haka. Sannan akan tanadi Kayan Aiki kafin a fara shi. Manya dai sukan yi wasan ne a dandali bayan an sha ruwa. Yara kuwa sukan shiga har cikin gida domin gudanar da shi.

8.4.1 Kayan Aiki

i. Kara mai ɗan tsayi

ii. Allo mai faɗi

iii. Ƙaramar tukunyar ƙasa ko randa ko wani abu mai kama da wannan

iv. Dogon jarbi

v. Kayan sawa na dattijai, wato babbar riga da hula da rawani

vi. Buzu

vii. Auduga (musamman ga yara domin su yi gemu da saje)

8.4.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su tanadi kayan aiki da aka ambata a ƙarƙashin 8.4.1. Ɗaya daga cikinsu zai yi shigar malami. Zai sanya babbar riga da hula da rawani. Sannan zai riƙe dogon carbi. Idan yaro ne za a nemi auduga a lilliƙa masa a fuska a matsayin gemu da kuma saje. Daga nan za a ɗebi sauran kayan aiki a ɗunguma wurin tashe.

Da zarar an isa wurin tashe, za a shimfiɗa buzu sannan wanda ya yi shigar malamai ya zauna bisa, ya harɗe. Sai kuma a gabato da sauran kayan aiki a aje nan gabansa. Shi kuwa yana harɗe ga shi riƙe da allo da kuma dogon carbi yana ta faman ja. Sauran masu wasa kuwa za su fara tambayarsa cikin waƙa, yayin da zai riƙa ba su amsa. Ga yadda abin yake:

Masu Tambaya: Boka kake ko malami?

Malam: A’a malam nake,

Ba boka ba ne ni.

Ga allo,

Ga kuma tauwada.

 

Ga carbina,

Ga kuma alƙalami.

 

Nan kuma butar rubutu,

In nai haka sai dai in haka,

In dage in juya haka,

In zauna in kuma yo haka.

 

Rubutu ne kowa ya gani,

Aikina dare da rana,

Awuni ashirin da huɗu.

Zai riƙa kwatanta duk abin da ya ambata. Wato zai riƙa tsoma wannan kara nasa cikin tukunyar ƙasa ko randa ƙarama da ke nan gabansa tamkar yadda almajiri ke tsoma alƙalami cikin tawada. Sannan zai yi ta faman rubutu bisa allonsa mai faɗi. Sukan kira wannan allo da suna allon saa. Duk wanda ya ba su sadaka, za su masa alƙawarin rubuta shi a allon sa’a. Wanda idan aka yi hakan, zai samu ci gaba a rayuwa.

8.4.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ƙwarai ga masu kallo. Sannan yana nuni zuwa ga wani abu da ke faruwa a ƙasar Hausa na game da malaman tsibbu da ke haɗa addini da kuma tsafi. An gina wasan bisa raha da ban dariya. Wannan alƙalami namalam kaɗai ya isa abin kallo.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments