Ticker

6/recent/ticker-posts

Gwauro

8.3 Gwauro

Wannan wasa ne wanda yake da sigar tashe. Ta wata fuska kuma za a iya bayaninsa a matsayin wasan da bai faɗa rukunin tashe ba. Dalilin da ya sanya ya yi kama da tashe kuwa shi ne, lokuta da dama akan ba wa masu wannan wasa abin sadaka.

Wasan gwauro ya sha bamban da sauran wasanni, domin kuwa ya fi kama da gaske. Za a yarda da hakan yayin da aka ga yadda shugaban gwauro wato Nalaku ya sa aka kamo gwauro aka shafa masa bula ko wani abin da zai masa fenti a fuska, sannan a masa kiɗa, kuma dole ya taka rawa. Adadin masu gudanar da wannan wasa na da yawa. Wani lokaci zai iya kai wa har arba’in ko ma sama da haka.

8.3.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Babu takamaiman wuri guda da aka keɓe domin wasan gwauro. Hasali ma sarkin gwauro da jama’arsa suna bi ne kwaroro-kwaroro da kuma dandali-dandali yayin gudanar da wannan wasa.

ii. Asalin wasan gwauro akan gudanar da shi ne da dare. Amma yanzu, musamman da yake abin ya sauya fuska, akan gudanar da wannan wasa har da rana. Sannan akan yi shi ba tare da kama gwauro ba. A maimakon haka, akan tafi ne ana kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙen habaici da zambo ga gwagware.

8.3.2 Yadda Ake Wasa

Kamar yadda aka nuna a sama, zamani ya yi tasiri kan wasan gwauro. Kullum akan samu sauye-sauye game da yadda ake gudanar da wasan. Asalin wasan dai ana gudanar da shi ne ƙarƙashin sarkin gwauro. Yayin da za a fita wasa, sarkin gwauro da mutanensa za su fita da kayan kiɗa da kuma ma kayan faɗa, irin su adda da wuƙa da sanda. Sai dai babu wanda za su doka da waɗannan kayan faɗa.

Sarkin gwauro zai sa a kama gwauro a ɗaura masa igiya a wuya ko a kunkumi, kamar wani biri. Sannan za a shafa wa gwauron abu a fuska kamar yadda aka bayyana a sama. Daga nan za a tafi da shi dandali ana masa kiɗa. Akan tilasta shi sai ya yi rawa.

Akwai waƙoƙi daban-daban da ake yi wa gwauro. Sun danganta da wurin da ake gudanar da wasan da kuma masu gudanarwa. Daga cikin misalan waƙar gwauro akwai:

Bayarwa: Gwauro-gwauro,

Amshi: Gwauro.

 

Bayarwa: Mai sahur da ƙarago,

Amshi: Gwauro.

 

Bayarwa: Buɗa baki da ƙanzo,

Amshi: Gwauro.

 

Bayarwa: Mai filo da katifa,

Amshi: Gwauro.

 

Bayarwa: Babu mata ɗaki,

Amshi: Gwauro.

 

 

Bayarwa: Babu butar salla,

Amshi: Gwauro.

 

Bayarwa: Mai jiƙonsa a leda,

Amshi: Gwauro.

 

Bayarwa: Gauro-gwauro,

Amshi: Gwauro.

Akwai wata waƙa kuma da sarkin gwauro da kansa yake rerawa, yayin da sauran mutanensa za su riƙa masa amshi. Ta kasance kamar haka;

Sarkin Gwauro: Sarki ya kama ɓarawo,

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: Ya manta da gwauro,

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: Wai ɓarayi ne ke da ɓarna,

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: An manta da gwauro.

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: Tunda sarki ke kamun ɓarayi,

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: Ni ko zan kama gwauro,

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: Wasa muka zo ba faɗa ba,

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: Mun zo mu kama gwauro,

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: Mai mata ba mai taɓa ka,

Amshi: Ga gwauro a titi.

 

Sarkin Gwauro: Amma za mu kama gwauro,

Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Ya yi azumi tara daidai,

Amshi: Cikinsu babu na zaɓe.

8.3.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallo da ba su faɗo rukunin gwagware ba. Domin an ce: “Faɗa ba da kai ba daɗin kallo.” Haƙiƙa wasan barazana ce ga dukkanin gwagware. Yana sanya duk wani gwauro ya yi himmar yin aure cikin gaggawa. Sannan yana nuna irin illolin gwaurantaka.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments