Ticker

6/recent/ticker-posts

Jatau Mai Magani

8.5 Jatau Mai Magani 

Wannan wasa na gama-gari ne tsakanin yara da manya amma maza. Yana ɗaya daga cikin wasannin tashe da ake gudanarwa a watan azumi, musamman da dare bayan an sha ruwa. Sannan ana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Adadin masu gudanar da wannan wasa sukan kasance uku zuwa sama da haka.

8.5.1 Kayan Aiki

i. Kwando ko daro ko wani abu makamancin wannan

ii. Layun wasa

iii. Ganyaye da saiwu da sassaƙe-sassaƙe

iv. Bula ko shuni ko wani abu mai kama da wannan

8.5.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su tanadi abubuwan da aka lissafa a sama. Sai kuma su zaɓi ɗaya daga cikinsu wanda zai yi shigar boka. Akan kira shi da suna Jatau. Zai sanya layu a jikinsa ko ta ina, amma nawasa. Ganyaye da saiwu da sassaƙe-sassaƙen da aka ɗebo kuwa, za a sanya su cikin kwando ko wani abun ɗauka. Daga nan za a ɗunguma, Jatau na gaba sauran masu wasa na biye.

Da zarar an zo wurin wasa, Jatau zai fara waƙa yayin da saura za su riƙa amsawa. Idan manya ne, sukan bi wuraren da ake taruwa ne domin hutawa, musamman bayan an sha ruwa. Yara kuwa sukan shiga har cikin gidaje. Ga yadda waƙar take:

Jatau: Jatau mai magani,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Sai ni mai magani,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kogo-gogo na shiga,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kogon kura na shiga,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kogon damusa na shiga,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kogon ɓauna na shiga,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Balle na maciji ɗan tsiya,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: To iya wanne za ki sha,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ko na ciki ko na haihuwa,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ko na korar kishiya,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Idan na baki na haihuwa,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Yau ki haifo sha biyar,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Gobe ki haifo sha biyar,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kin ga talatin sun cika,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kafin wata ɗaya zahiri,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kin tara ‘ya’ya ɗari,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Idan na baki na kishiya,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Larai ta zo ta fita,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Maimuna ta zo ta fita,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Laraba ta zo ta fita,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kafin sati ko guda,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Kin kore mata ɗari,

Amshi: Jatau.

Waƙar wannan wasa tana da faɗi. Domin kuwa akan samu sauye-sauye cikin yadda ake rera ta. Wannan ya danganta da wuri da kuma masu wasan. Misali waƙar da aka kawo a sama, yara ne suka fi amfani da ita. Domin ciki ana magana ne kai tsaye da matan aure. Manya kuwa da ke gudanar da nasu wasan a waje, akan samu canji cikin salon waƙarsu. Misali akwai inda suke cewa:

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ka ga wannan gwanda ce,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ko da ba ya magani,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ko don zaƙi za ka sha,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ka ga wannan zogala,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ko ba ya magani,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: In an yi kwaɗo ai za ka ci,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ka ga wannan yakuwa,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Ai ko ba ta magani,

Amshi: Jatau.

 

Jatau: Za a yi taushe za ka sha,

Amshi: Jatau.

Haƙiƙa a wannan waƙa ta biyu, za a ga cewa da maza ake, musamman magidanta.

8.5.3 Tsokaci

Wannan wasa yana nishaɗantarwa ƙwarai musamman ga masu kallo. Sannan yana ɗauke da saƙwanni daban-daban a cikinsa. Yana nuna wata al’ada ta Bahaushe da ta danganci cuta da neman magani. Sannan yana fito da wata halayyar mata ta neman magani domin kishi a gidajen aure. Baya ga haka, waƙar wasan na ɗauke da wani kurman baƙi da ke nuni da cewa, ba fa kowane magani ba ne na gaske. Domin Jatau da kansa ya nuna cewa, ko ma dai bai yi maganin ba, ai zai yi wani amfani na daban.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments